✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Lemon kwalba Wani Bafulatani ne ya je shagon mai sayar da lemon kwalba sai ya ga kowa idan za a miko masa sai an bude…

Lemon kwalba

Wani Bafulatani ne ya je shagon mai sayar da lemon kwalba sai ya ga kowa idan za a miko masa sai an bude kwalbar. Shi ma da aka bude masa sai ya ce wa mai lemon nawa ne, ya ce masa Naira 60. Bafulatanin ya ce: “Kai amma ya yi tsada gaskiya, a zuba mini na Naira ashirin a leda.”

Daga Garba Sabiyola Gashuwa, 08096284154

 

 

Neman total

Wani Bahadeje ne yana aikin baranta a gidan masu kudi sai ran nan Hajiya ta ce: “Danhadeja za ka iya zuwa kasuwa?” Ya ce mata: “Eh mana, haba Hajiya, kasuwa kuma ai na zama dan gari tunda na gane komai yanzu.” Hajiya ta ce bari ta rubuta masa abubuwan da zai sayo a takarda. Ta rubuta masa kamar haka: Magi-N200, gishiri-N100, albasa-N100, tarugu-N100, kori-N100, manja-N250. A kasa sai ta rubuta Total (Jimilla) -N850, ta mika wa Danhadeja ya tafi kasuwa. Duk ya sayi komai amma ya yi ta yawo a kasuwa wai shi yana neman Total. Hajiya ta gaji da jira ta kira shi a waya: “Kai Danhadeja ina kake tun dazu ba ka dawo ba, lafiya, ga shi yamma na yi?” Sai ya ce mata: “Wallahi na sayi komai, ya rage Total ne kawai Hajiya, yanzu ma na samu wani bawan Allah ne zai nuna mini inda zan samu Total!”

Daga Iliyas Idris Fahad Suleja

 

 

Fusatanwar mata

Wani matashi ne ya fito waje, domin matarsa ta bata masa rai, ashe bai sani ba shi ma mahaifiyarsa ta bata wa babansa rai kuma a daidai lokacin bai san cewa baban nasa yana bayansa ba. Matashin nan sai ya ce: “Allah Ka la’anci mata amma ban da mahaifiyata.” Jin haka sai babansa ya yi wuf cikin fushi ya ce: “Hada da ita, ai ita ce ma babbar la’ananniya.”

Daga Amiru Isa Bakori, 08075959086

 

 

Bahadeje da keke

Wani Bahadeje ne ya hau keke, yana cikin tafiya sai ya hadu da wadansu yara. Daya daga cikinsu ya kalle shi ya ce: “Allah Sarki, kun ga wani mutum a kan keke yana tafiya, wilinsa yana juyawa!” Ashe Bahadeje yana jin su, nan da nan sai ya sauka daga keken ya yi ta turawa har ya je wajen mai gyara ya ce masa: “Ina tafiya ne a keken nan sai wili ya fara juyawa.”

Daga Abban Fiddausi, 08034463170