✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Wani mahaukaci ne ya fito yawo kasuwa ba wando ba riga! Kawai sai ga wani mahaukaci shi ma ya zo sai na bayan ya hango…

Wani mahaukaci ne ya fito yawo kasuwa ba wando ba riga! Kawai sai ga wani mahaukaci shi ma ya zo sai na bayan ya hango dayan, ba riga ba wando,  ya yi maza ya kamo hannunsa ya kwada masa mari.Ya ce duk irinku ne kuke ja mana zagi a gari. Sai ya kwabe kayan jikinsa ya ba shi ya sa, shi kuma ya yi tafiyarsa tsirara!

Kabir Abubakar Kusfa, Kaduna 07088899855

 

Wani mahauci ne aka kai shi kotu a kan bashi, alkali ya yanke masa hukuncin daurin wata shida. Za a fita da shi zuwa kurkuku sai alkali ya ga bakinsa na motsi yana fadin wani abu a boye. Sai alkali ya ce: “Ina fata dai ba zagina kake yi ba ko?” Sai mahauci ya ce: “Amma dai kuma ka san ba yabonka nake yi ba!”

Daga Mudassir Ibrahim Mando Jihar Kaduna  08034371602

 

Wani saurayi ne ya shiga motar haya sai ya hadu da wata kyakkyawar budurwa, kuma ya rasa yadda zai yi mata magana. Domin ya burge ta sai ya ciro wayarsa ya sa a kunne yana cewa ‘Halo momi wallahi ba zan samu damar zuwa ba, ki ba kanena ya kai masa Naira miliyan 25 yanzu. Ina hanya zan tafi gidan Gwamna wata ganawa.’ Bayan ya gama wayar sai ya ga budurwar tana kallonsa. Sai ya ce yaya aka yi? Sai ta ce tun dazu nake so in fada maka kana ciro wayarka sai batirinta ya fado ga shi can kasa!

Daga 09092969381

Kamar ni, kamar ba ni ba!

 

Wani Bafulatani ne ya kai shanunsa kasuwa ya sayar ya sayi kosai don yin guzuri, ya kulle sauran kudinsa a jaka ya kama hanyar gida. Yana cikin tafiya sai ya zo gindin wata bishiya ya fito da kosan ya ci, yana gama ci barci ya dauke shi. Sai barayi suka lallabo suka sace jakar kudin, sannan suka yi masa aski. Can ya farka ya ga babu jakarsa, sai ya fasa ihu ya dora hannunsa a kai, sai ya ji babu suma. Sai ya ce, “Kamar ni, kamar ba ni ba! Ashe ba ni ba ne!”

Sabi’u Mai Mai, Kofar Mazugal, Kano

08097379652