✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Bari in bi su ko da gaske ne! Wani mahaukaci ne ya iske yara suna wasan kasa sai ya ce kai ku je can ana…

Bari in bi su ko da gaske ne!

Wani mahaukaci ne ya iske yara suna wasan kasa sai ya ce kai ku je can ana raba Naira-Naira. Sai yaran suka tafi da gudu, sai mahaukaci ya ce kai bari dai in bi su ko da gaske ne! 

 

Saniya da ciki ma ta mutu

Wani Bafulatani ne mahaifiyarsa ta rasu sai Sarkin Pawa da jama’arsa suka je yi masa ta’aziyya. Bayan sun gaisa sai Sarkin Fawa ya ce da Bafulatanin sai ka yi hakuri ka san rashin mahaifiya babban rashi ne. Sai Bafulatanin nan ya ce haba Sarkin Fawa? Yo Sarkin Pawa, saniya da ciki ma ta mutu mun yi hakuri balle Inna!

 

Liman da kura

Wani limami ne ya fito zuwa masallaci da Asuba sai ya ji mutane sun taho a guje suna cewa jama’a ku tare mana ita kada ta gudu. Liman yana waiwayawa sai ya ga kamar akuya, sai ya yi wuf ya kunshe ta da babbar rigarsa. Mutanen suna zuwa sai daya daga cikinsu ya ce da liman amma Baba ka cika jarumi. Sai Liman ya ce yaro ai tun ina yaro ni jarumi ne. Sai mutumin ya ce wa dan uwansa miko min takunkumin nan in sanya mata. Sai Liman ya ce yaro me na kama ne? Sai ya ce ai kura ce Baba! Kafin ya karasa fadi har liman ya fadi kasa a sume!

 

Wayyo Babana ne!

Wani dan jarida ne yana cikin tafiya a sai ya ga an taru a wurin wani hadari. Ya je da nufin ya dauki rahoto amma an cika sosai, ya yi, ya yi a matsa masa aka ki sai ya ja da baya ya kwala ihu. Ya ce wayyo Allah! Ku buda min Babana ne ku matsa in yi masa kallon karshe! Mutane suna jin haka sai suka matsa yana zuwa sai ya ga ashe jaki ne mota ta kade!

Labarai daga Daga 09092969381

 

Ga baturin wayarka nan a kasa

Wani saurayi ne ya shiga motar haya sai ya hadu da wata kyakkyawar budurwa, amma ya rasa yadda zai yi mata magana. Domin ya burge ta sai ya ciro wayarsa ya sa a kunne yana cewa ‘halo momy wallahi ba zan samu damar zuwa ba ki ba kanena ya kai masa Naira 25 yanzu. Ina hanya ce zan tafi gidan Gwamna wata ganawa. Bayan ya gama wayar sai ya ga budurwar tana kallonsa. Sai ya ce mata yaya aka yi? Sai ta ce tun dazu nake so in fada maka kana ciro wayarka sai baturinta ya fado ga shi nan a kasa! 

Labarai daga 09099886988