✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu ne ruwan jakara – a sha a birni, a sha a kauye

Talata 5 ga watan Oktoba, 2021 ake bikin Ranar Malaman Makaranta ta Duniya. A wannan rana ce a fadin duniya hukumomi da makarantu da masu…

Talata 5 ga watan Oktoba, 2021 ake bikin Ranar Malaman Makaranta ta Duniya.

A wannan rana ce a fadin duniya hukumomi da makarantu da masu ruwa da tsaki a harkar koyo da koyarwa, musamman wadanda suka hada da su malamai kansu da dalibai da gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu da ’yan jarida da dai sauransu, suke shirya ko halartar tarurruka na musamman domin bayyana muhimmancin malami wanda shi ne kashin bayan ilimi.

Shi dai malami wata babbar korama ce wadda za a iya cewa ruwan jakara ne, ko a sha shi a birni ko a sha shi a kauye.

Duniya ta jima da fahimta da kuma amincewa cewa babu wani ruwa da yake gusar da kishirwar kowa da kuma dattin jikin kowa da ya wuce ilimi, kuma babu shakka duk mutumin da ke raye da wuya ya ce ba shi da malami ko bai amfana da malami ba.

Wannan na cikin dalilan da suka sanya ake yi wa malamai kirari da cewa su ne magada annabawa.

A irin wannan rana ce ta tunawa da hidimar da malamai suke yi wa al’umma wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware a duk shekara a sassan duniya, musamman kasashen da suka ci gaba, ake shirya tarurruka don tattauna ina aka fito ko kuma ina ya kyautu a dosa don kyautata rayuwar malamai da kuma fito da sababbin dabaru ko hanyoyin da za a inganta ilimi da kuma harkar koyo da koyarwa.

Ba boyayyen lamari ba ne cewa a duk sassan duniya, al’ummomi da gwamnatoci sun gamsu da cewa malamai su ne jigon rayuwa kuma su ne tsanin kawo wa  al’ummar kowacce kasa ci gaba.

Ma’aunin cigaba

La’akari da wannan tasiri na malamai da kuma ilimi a cikin al’umma ne, wasu masana da masu hangen nesa suke bayyana cewa babban madubin auna ci gaban kowacce kasa, ko kuma al’umma, bai wuce a haska fitilar nazari da bincike kan irin hali ko kuma yanayin da malaman wannan kasa ko al’umma ke ciki ba a matsayin ma’aunin dogaro.

Babban abin tambaya dai a nan shi ne, wai mene ne ke sanyawa duk da cewa ba a da wani sauran kokwanto game da tasiri ko matsayin malamai wajen zama babbar gadar haifar da ci gaban rayuwar mutane a daidaikunsu da ma a kungiyancensu, a matsayin al’umma, amma kuma ba a ba su muhimmancin da ya kamace su?

Shin ba malaman ba ne har a yau magada annabawa kuma jirgin fiton al’umma da kawo musu ci gaba?

Idan dai har yau malamai su ne jigon cigaba, me ya sanya hakan bai hana gwamnati da sauran mutane musamman a kasashe kamar Najeriya, wato kasashe masu tasowa, ci gaba da yi wa malamai rikon sakainar kashi da kallon raini da kuma yi musu shakulaton bangaro ba, musamman a fagen lura da jin dadinsu ko walwala ko kuma inganta rayuwarsu?

Babu shakka hakan ba ya rasa nasaba da irin rashin kyakkyawar kulawa da hukumomi da gwamnatoci ke wa harkar ilimi duk da kwana da sanin alfanunsa da muhimmancinsa da kuma tasirinsa wajen haifar wa kasa da kuma al’umma cigaban da take mafarki da kuma tsananin bukata.

A Najeriya, musamman bayan da Ministan Ilimi mai ci, Malam Adamu Adamu, ya kama aiki, gwamnatinsa ta yi ta ikirarin fito da sababbin hanyoyin kyautata rayuwar aiki ga malaman makaranta don inganta albashinsu da kuma samar musu da yanayin aiki mai kyau domin yin aiki cikin nishadi da walwala.

Holoko, hadarin kaka

Amma dai har ya zuwa yau, malaman Najeriya za su iya cewa duk da hadarin alheri da aka ce musu ya gangamo, hadarin ba shi da bambanci da hadarin nan da ake cewa holoko hadarin kaka, domin ta kare ne da aka ce wai ana biki a gidan su kare, sai ya ce in gani a kasa.

Shin yaushe wannan hadari zai fara zubar da ruwa, malaman Najeriaya su sha kuma su yi wanka? Masu hikima dai na cewa lokaci shi ne babban alkali.

An dai ce wai an kara wa malaman makarantun firamare da na sakandare shekaru biyar kan shekaru talatin da biyar na ka’idar aiki da duk sauran ma’aikata su ke yi, kuma an yi al’kawarin kyautata musu albashi.

Shin wannan alkawari da mafarkin malaman na samun rayuwa mai kyau ta hanyar morar sabon tsarin albashi, zai kai ga duk malamai masu koyarwa a matakin jihohi da kananan hukumomi ko kuwa rijiya za ta bayar guga ya hana?

Wadanne matakai gwamnatin tarayya ke kokarin dauka don tabbatar da cewa in har ruwan saman wannan sabon albashi ya fara zuba ba zai tsaya ga malamai masu aiki a matakin tarayya kawai ba?

Kuma wanne kokari gwamnatoci a duk matakai suke yi don magance rashi da kuma karancin kayan aiki da malamai ke fama da su a kusan dukkan makarantun gwamnati da ke fadin Najeriya musamman a wannan Ranar Malamai ta Duniya?

Ko kuwa da za a ci gaba da abin nan ne da ake cewa ana fakewa da guzuma ana harbin karsana, wato ana karyar inganta rayuwar malamai da harkar koyo da koyarwa domin fidda makudan kudade amma kuma ana arzuta kai?

Da yake an jima ana yi wa malamai a Najeriya abin nan da masu hikima ke cewa gafara sa, amma ba su ga kaho ba, lokaci dai shi ne ke bayyana gaskiyar kurma – ko alkawarin Malam Adamu Adamu na inganta rayuwar malaman zai zama gaske, ko a’a.

Khalid Imam marubuci ne kuma malamin makaranta.