✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu muka harbo jirgin yakin Najeriya —Boko Haram

Ta fitar da bidiyon mushen jirgin yakin da gawar daya daga cikin matukansa

Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin yakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ake nema tun ranar Laraba.

Kungiyar ta fitar da wani bidiyo a yammacin ranar Juma’a wanda a ciki ta nuna wani mushen jirgin yaki mai dauke da tutar Najeriya da kuma lambar Rundunar da kuma gawar daya daga cikin matuka jirgin.

Boko Haran ikirarin mayakanta ne suka baro jirgin, amma wasu kwararru na tantamar ko kungiyar na na karfin kakkabo jirgin yaki daga maboyarta.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, kakarin Rundunar, Edward Gabkwet, ya bayyana sunayen matuka jirgin amma bai yi karin bayani ba.

Wani mayakin Boko Haram a kan jirgin yakin da kungiyar ke ikirarin ta harbo.

Kawo yanzu dai Rundunar ba ta ce uffan game da ikirarin kungiyar ba.

A cikin bidiyon an ga wasu mayaka a kan babura da motocin yaki suna tafiya a wari wuri da kura ta turnike.

Ya kuma nuna jirgin ya yi bindiga a sararin samaniya kafin ya fado, sannan daga karshe aka ga wani mayaki dauke da bindiga fuskarsa a kan mushen jirgin.

Mayakin ya ce, “An turo jirgin yaki na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya mai lamba 475 zuwa Sambisa ya yaki Mujahidai.

“Ba mai iya yaki da Allah, ga kuma shaidar abin da Allah Ya yi. Ba yadda za ku yaki bayin Allah ba tare da irin wannan ya faru ba,” inji shi cikin harshen Turanci.