✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu koyi darasin rayuwa daga labar 01in kwadi biyu

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta bibiyar filin Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, yau kuma mun zakulo wani tsohon labari ne, wanda ke cike da darussan rayuwa,…

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta bibiyar filin Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, yau kuma mun zakulo wani tsohon labari ne, wanda ke cike da darussan rayuwa, musamman ma ta fuskar turzawa ko yin kokari a rayuwa.
Labarin dai ya kasance ne na wasu kwadi guda biyu, daya yana da kiba sosai, daya kuwa ramamme ne, marar kumarin jiki. Wata rana suna kiciniyar neman abinci a wani kamfanin yin madara, sai kaddara ta sanya suka fada cikin wani durum din madara. Suka yi kokarin su fita daga cikinsa, amma dai suka kasa, musamman saboda gefen durum din santsi ke gare shi, don haka duk yunkurin da suka yi domin fita, sai santsin nan ya tadiye masu kafafu su sake fadawa.
Suna cikin kiciniyar fitowa, sai kwadon nan mai kiba ya ce wa ramammen: “Ya kai dan uwana, ina ganin mu daina bata lokacinmu a banza, domin kuwa mun riga mun halaka. Mu daina yin wani kokarin fita, domin kuwa babu wata hanya da nake ganin za mu kubuta.”
Shi kuwa ramammen kwadon nan, kasancewarsa mutum mai kokari, sai ya ce wa dan uwansa: “A’a dan uwana, kada mu karaya, mu ci gaba da tagazawa, babu mamaki mu samu mu kubuta daga wannan wuri. Kada mu fitar da tsammani, wani na iya zuwa ya cece mu, don haka kada mu zauna haka cikin madara har ta kai ga halaka mu, mu ci gaba da yunkuri.” Haka suka ci gaba da yunkurawa, suna tsalle, suna komawa cikin durum din madarar nan har zuwa tsawon lokaci.
Bayan wani lokaci, sai kwadon nan mai kiba ya kara karaya, ya ce wa dan uwansa: “Ni dai na saduda, na gaji likis, kuma sai kara gajiya nake yi. Ni dai zan daina wannan yunkuri kawai, domin kuwa yau kamfanin nan babu kowa, tun da yau Lahadi, da wuya a ce wani ya zo ya cece mu. Mu dai mun halaka, ba mu da wata hanyar kubuta.”
Shi kuwa ramammen kwadon nan mai kokari da himma sai ya ce wa dan uwansa: “Kada mu karaya, mu ci gaba da kokari, domin kuwa mai nema na tare da samu.” Nan fa suka ci gaba da kiciniya da kokarin fita daga cikin madarar nan.
“Wayyo Allah! Ni dai na gaji, ba zan ci gaba da wani yunkuri ba. Ni dai ina ganin babu wani amfanin badi babu rai, domin kuwa lalai ruwan madarar nan zai halaka mu ne kawai.” Inji kwado mai kiba, kuma yana gama fadin haka, sai ya yi lakwas, ya yi lamo cikin ruwan madara. Kafin ka ce kwabo, ya ce ga garinku nan, ya halaka. Shi kuwa ramammen kwadon nan, da ya ankara da haka, maimakon ya karaya, sai ya kara himma, ya yi ta tsalle, yana turzawa da nufin fita daga kwanon madarar.
Yana cikin wannan kiciniya, sai kawai ya ji kafarsa ta taka wani dunkulen madara. Ashe a sakamkon wannan tirjiya da yake yi, wani sashen ruwan madarar ya daskare, don haka da ya taka, sai ya yi wani kakkarfan yunkuri, ya yi tsalle; sai ga shi facal a waje. Allah Ya taimake shi ya kubuta daga halaka, ya fice daga durum din madarar.
Ya ku masu karatu, ina fata mun fahimta da darasin rayuwar da wannan labari yake koya mana. Bari in dan kara ta’aliki, domin darasin ya kara fitowa sarai. Wannan labari, kamar yadda muka gani, yana koya mana muhimmancin mikewa da turzawa da yin kokari domin neman abin da mutum yake bukata. Idan mun lura, shi ramammen kwado, ya kasance mai yin himma da kokarin neman mafita, wanda dalili ke nan ya samu nasara. Shi kuwa dayan ya kasance raggo, malalaci, wanda haka ya sanya ya halaka.
Haka kuma, labarin nan na nuna mana tasirin kyautata zato da kyautata tsammani. Idan mun lura, shi ramammen kwado ya kasance mai kyautata tsammani da nuna rashin karaya. A duk lokacin da ka samu kanka kana yin wani abu, idan ka sanya himma kuma ka kyautata tsammani, babu shakka akwai yiwuwar samun nasara. Mu dubi dai yadda kwado mai kiba ya halaka, kawai saboda ya kasance malalaci kuma mai yanke tsammani.
Wani darasi kuma da za mu kara fahimta daga labarin shi ne, yana da kyau mutum ya kasance mai jin shawarar dan uwansa, musamman mai kyau. Mu dubi yadda ramammen kwado ya yi ta ba dan uwansa shawarar cewa kada su karaya, su ci gaba da kokari, amma ya yi kunnen uwar shegu da shawarar. Da a ce ya ji wannan shawara, babu mamaki shi ma da ya tsira, kamar yadda dan uwansa shi ma ya kubuta.
Don haka, duk inda muka samu kanmu, mu kasance masu kokari da sa himma ga duk abin da muka tunkara. Mu kasance masu kyautata zato da kyautata tsammanin samun nasara ga al’amari, ba asara ba. Haka kuma, lallai ne mu kasance masu jin shawarar abokan zamanmu, ba masu yanke kuduri da tunanin kanmu kadai ba. Allah Ya sa mu dace, amin.