Ramamme haukata kato
Sa mutum ya mari jikinsa
Mugu hana barci
Wannan shi ne kirarin da a kai ma sauro a cikin littafin nan na Hausa mai koyar da tsafta ga daliban makarantun Firamaren tsohon lardin Arewa, mai suna Bala da Babiya. Wannan batu kuma shi ya kawo ni akan batun blkin ranar cutar zazzabinciwon sauro ta duniya da ake yi a kowace ranar 25 ga watan Afrilun kowace shekara a kasashen da suke cikin Majalisar dinkin duniya. Cutar da a yau, ba sai gobe ba, ita ke kan gaba wajen mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara a duk fadin duniya. kiddigar shekarar 2012, ta tabbatar da cewa mutane 627,000, suka mutu a wannan shekarar a sanadiyar cutar ta zazzabin cizon sauro, kuma akasarinsu daga nahiyarAfirka. kasar nan da kasar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo kuma suke fama da kashi 40 cikin 100, na mace-macen.
Masana ilmin kiwon lafiyar dan Adam, sun yi ittifaki akan cewa wannan dan karamin kwaro, wato sauro da ba a iya ganin cikakkiyar halittar sa, har sai an yi amfani da madubin nan na gwaje-gwaje da ake kira microscope da kan kara girman halitta, shi ke haifar da wannan cuta ta zazzabin cizon sauro.
A watan Mayun 2007, a zaman Majalisar dinkin duniya, na 60, Majalisarta zartas da a rinka bikin ranar da aniyar ilmantar da fadakar da al`umma illolin wannan cuta, da irin matakan da za su rinka dauka don kare kansu.
Kodayake kafin zartas da wannan kuduri kasashen Nahiyar Afirka sun fara bikin ranar cutar ta zazzabin cizon sauroa ranar 25-04-2001, shekara daya bayan kasashen sun yi wani kasaitaccen taron a Abuja mai taken “Yaki da cutar zazzabin ciwon sauro na duniya” wato Roll back Malaria Partners a karkashin shirin Muradan karni, inda kasashen Nahiyar 44, da tallafin kungiyar Lafiya ta Duniya, wato WHO da Asusun tallafa wa kananan yara na Majalisar dinkin Duniya, wato UNICEF da ita kanta Majailasar dinkin Duniyar, kasashen suka rattafa hannayensu akan yarjejeniyar yaki da cutar.
Taken bikin ranar na bana shi ne “Hada karfi wuri guda a yau da tunanin gobe, don kakkabe cutar baki daya.” kasar nan ta yi bikin bana a babban birnin jihar Abia, wato Umuahia, a karkashin jagorancin Ministan kiwon lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu, wanda ya fada wa manema labarai cewa kasar nan ta yi gagurumar nasara a cikin yaki da cutar, kuma za ta ci gaba da yin hakan, ta hanyar ci gaba da kashe makudan biliyoyin Nairori, har zuwa lokacin da za ta kakkabeta baki daya. Wannan yakin na kowa da kowane, don haka sai kowa ya kama za a kai ga cimma nasara.
Kafin in dawo kan maganar Minista akan kowa sai ya kama, ta yadda za a iya kakkabe wannan cutar. A kasar nan ita ce kan gaba a kasashe masu fama da cutar 106, kasashen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Baurki Faso da Saliyo da Mozambik, na bi mata cikin kasashe 106. An kiyasata cewa daga cikin mutane miliyan uku da rabi, da suke kamuwa da cutar a shekara a wadancan kasashe, kasar nan da ta Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo suke da kashi 40 cikin 100, na wancan adadi. Yayin da kashi 97 cikin 100, na al`ummar kasar nan suna cikin barazanar su iya kamuwa da cutar. Haka kuma kashi 60 cikin100, na masu ziyarar asibitoci a kasar duk shekara sukan je ne kan neman maganin wannan cuta ta zazzabin cizon sauro.
Akan mace-mace kuma daga cikin wancan adadi na mutane 627,000, da suke mutuwa a shekarar 2012, akan cutar, kusan dubu uku, wannan adadin mace-mace ya zarta da mutane dubu 100 akan mutanen da suke mutuwa akan mummunar cutar nan mai karya garkuwar jiki ta HIb/AIDS, duk shekara.
Kan waccan magana ta Ministan, ta sai kowa ya kama za a iya kakkabe cutar anan kasar. Masana kiwon lafiyar bil Adam din dai sun tabbatar da cewa cutar zazzabin cizon sauro cuta ce da sauron ke yadawa daga irin kazantar da yake ci ya rayu, kazantar da idan ka duba, ba inda bamu fama da ita,kama daga zuwa makudan ruwanmu da na gidajenmu daban dakunanmu da kusan dukkan mahallinmu, ta yadda ba mu da wurin a yau, wa-lau a biranenmu ko kauyukanmu da za ka ce sun tsira daga wuraren hayayyafar sauro.
Samun tsaftataccen muhalli shi ne babban rigakafin da za mu iya kakkabe cutar zazzabin cizon sauro a kasar nan, kafin ka yi maganar kwanciya a cikin gidan sauro mai magani (gidajen sauron da ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da taimakon kungiyoyin bayar da taimako na duniya suka samar da miliyoyinsu kyauta). Akwai kuma bukatar a rinkafeshin maganin sauro a magudanan ruwa da dukkan inda ruwa yake kwanciya da gidajenmu da kasuwanninmu, ba don komai ba nake fadin haka sai don ita cutar ta zazzabin cizon sauro, cuta ce da rigakafinta ya fi maganinta arha da biyan bukata.
Magungunan da muke sha ada don samun waraka daga wannancuta, kamar irin su Kuni mai tsanin dacin nan, tuntuni Turawa masu shigewa gaba akan kiwon lafiyarmu suka ce ya daina.
Ina ga lallai akwai bukata mutanen kasa mu kula matukar kulawa wajen daukar rigafi, mu da kanmu, musamman kyauta tsaftar muhallinmu, ya yin da mahukunta tun daga kasa har sama su kuma su himmatu wajen fadakarwa da samar da gidajensauro wadatattu da zuba idanu suna kwashe shara da yin feshi a duk inda ya kamata, ta haka ne kawai za mu shiga sahun kasashen da suka ci gaba wajen raba kanmu da wannan.