✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu gana a chamba

Wani Bafulatani ne ya kai kara kotu. Bayan an kare shari’a sai alkali ya ce masa: “Mu hadu a chamba mu gana.” Ashe Bafulatanin ya…

Wani Bafulatani ne ya kai kara kotu. Bayan an kare shari’a sai alkali ya ce masa: “Mu hadu a chamba mu gana.” Ashe Bafulatanin ya sayar da shanu biyu, wajen a gana da alkali sai da kudin suka kare. Ko da ya fito sai dan uwansa ya ce masa: “Yaya kun gama?” Sai ya ce: “Kai bari, ashe ‘bari mu gana’ shegiya ce, duk ta cinye kudin shanu biyu.”

Daga Abdullahi Muhammad