✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu duba darasin da ke cikin hikayar nan

Assalamu alaikum ya ’yan uwana. A yau kuma za mu shiga wani maudu’i ne wanda nake ganin za mu karu da shi sosai, musamman idan…

Assalamu alaikum ya ’yan uwana.
A yau kuma za mu shiga wani maudu’i ne wanda nake ganin za mu karu da shi sosai, musamman idan mun tsaya tsam da ranmu muka yi nazarin darussan da ke cikinsa. Na san da dama daga ma’abota sani, sun dade da sanin wannan hikaya da zan kawo, don haka sai ta zama kamar tunatarwa. Ga wadanda ba su taba jinta ba kuwa, to sai in ce a taya ni nazari, domin kuwa ita rayuwa da kuma harkar ilimi yawa gare ta kamar kasar Subuhana. Kuma kamar yadda na sha nanatawa a wannan fili, ba wai samun ilimi ko gargadi ne fa’ida ba, babbar fa’ida na nan tsaye wajen aiki da shi. Domin kuwa, duk ilimin da ya taru, amma babu aiki da shi, to kamar jaki ne da aka dibga wa kayan littattafai, wadanda na tabbata ba za su amfane shi ba. Don haka ga hikayar nan tafe:
A can zamanin da mai nisa, akwai wani dattijo mai tsananin hikima da basira. Dattijon ya kasance mutum mai tsananin tsoron duniya, kuma ga shi ma’abucin ilimi; don haka yake taka-tsan-tsan da al’amuran rayuwa. Ga shi dai ya tsufa, amma yana tare da karfin zuciya, kuma yana da da guda daya, wanda ya dade yana tarbiyantar da shi bisa hanya ta kwarai.
Rannan sai ya kira dan nasa, ya ce masa su shirya za su tafi unguwa, amma ya ce masa duk inda suka je, ya saurari abin da mutane za su ce game da su. Ta nan zai koyi wani babban darasi na rayuwa. Haka kuwa suka yi, sai tsohon nan ya kwabe jakinsa, ya tasa dansa gaba suka shiga tafiya.
A karo na farko, sai ya ce wa dan nasa kada su hau jakin nan, sun dai tasa shi gaba suna korawa. Kan haka har suka zo daidai gungun wasu mutane, wadanda nan take suka fara magana game da su. Sai ya ce wa dan nasa ya saurara da kyau ya ji abin da suke fada. Shi kuwa yaro sai ya ji suna cewa: “Kai, yau ga wasu wawayen mutane, ku dubi yadda suke kora kosasshen jaki haka nan! Su ba su san cewa an yi musu ne don su hau ba, ga shi duk sun gaji da tafiya, shi kuwa jakin ko oho?”
Jin haka, sai tsoho ya ce, “ka ji abin da suke cewa ko?” Yaro ya ce ya ji. Sai ya ce, “to mu ci gaba da tafiya.” Sun ci gaba da tafiya, sun bace daga mutane, sai tsoho ya ce su hau jakin gaba daya. Nan take suka dare bayan jaki su biyu, suka kora abinsu suna ta tafiya har suka kawo wajen wasu mutanen na daban.
“Kai jama’a, ku dubi wasu mutane marasa tausayi! A ce mutum biyu katta-katta da ku amma ku dare bayan jaki daya, ko an gaya musu shi dabba bai da rai ne?” Inji wani mutum da ke kallonsu. Dattijo ya sake jawo hankalin dansa, ya ce ya ji abin da suka ce? Yaro ya amsa cewa ya ji. Bayan sun wuce sun je gaba, inda babu mutane, sai ya ce su sauka. Bayan sun sauka, sai tsohon ya ce wa dansa shi ya hau jakin shi kadai. Yaro ya dare jaki, tsoho ya bi bayansa yana kora masa.
Suna tsakar tafiya, sai suka kawo wajen wasu mutane kuma, sai suka ji wani na cewa: “Amma dai yaron nan bai da tausayi, dubi yadda ya hau jaki shi kadai ya bar tsoho a kasa yana ta shan wahala. Duniya dai ta lalace, ba a daratta na gaba.”
“Ka ji abin da wadannan suka ce ko?” Tsoho ya tambayi dansa. Shi kuwa ya amsa masa da cewa, ya ji. Suka ci gaba da tafiya, bayan sun bace wa mutane, sai yaro ya sauka tsoho ya hau jaki shi kadai, alhali yaro na korawa. Suna zuwa wajen gungun wasu jama’a sai suka ji wani yana gulma da su; yana cewa, wai tsohon bai da tausayi, maimakon ya bar dan ya hau jaki, ko kuma su hau gaba daya, amma sai shi kadai ya haye abinsa? Nan ma tsoho ya nusar da dansa abin da suka ce, yaro dai ya ce ya ji.
Bayan sun bace wa jama’a, sai tsohon ya ce to bari su dauki jakin a ka. Nan fa suka daure jakin nan tamau, suka nada gammo suka dauke shi a kawunansu. Suna tafiya har suka iso kusa da mutane. Nan take mutane suka yi masu zobe, suna ta kallon abin al’ajabi. Wani daga jama’ar na cewa: “Yau kuma ga abin mamaki! Anya wadannan ba mahaukata ba ne ba? Yaushe mutane za su dauki jaki a ka, maimakon shi da ya kamata ya dauke su?” Shi kuwa tsoho bai ce wa kowa kanzil ba, har sai da suka wuce wurin mutanen. Daga nan ya ce wa yaro ya ji abin da mutanen suka ce ko? Yaro ya ce, ya ji.
“To, ina son ka yi amfani da hankalinka, ka kuma yi amfani da abubuwan da suka faru da mu a cikin wannan tafiya. Nan za ka gane cewa, ba za ka iya gamsar da mutane ba, kuma ba za ka iya yi wa kowa daidai ba.” Inji tsoho ga dansa. Ya ci gaba da cewa, “don haka ya kamata ka kula da al’amuran rayuwa, duk abin da za ka yi, ka tsaya kan hakikanin gaskiya, kada ka damu da abin da mutane za su ce, muddin dai kana kan gaskiya. Domin idan ka biye ta maganar mutane, to ba za ka iya ma aikata abin da ka yi imani da shi ba. Ke nan ya dace ka lura da abin da ya faru gare mu a wannan tafiya da muka yi da jaki. Kowa da ra’ayinsa, to wanne za mu bi?”
Tun daga lokacin nan, yaro ya koyi darasin rayuwa cikin al’umma. To, ni ma a yau, ina jawo hankalinmu da mu lura da fasahar da ke cikin wannan labari, mu yi aiki da shi, domin zai taimaka mana. Ko me za ka yi, ka yi tsaka-tsaki, kada ka wuce, kuma kada ka gaza. Ko kyauta za ka yi, kada ka yi domin jama’a su yabe ka ko kuma don gudun kada mutane su zage ka. Rayuwa dai wahala gare ta, dole sai da taka-tsan-tsan. Ta masu iya magana, da suka ce, ruwa a cokali, ya ishi mai hankali wanka!