✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu ba ‘yan kala kato ba ne, ‘yan Kur’aniyun ne -Usman Yakubu

A karshen makon nan ne jami’an tsaro suka kai samame a wani gida da ke Farakwai a cikin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna inda…

A karshen makon nan ne jami’an tsaro suka kai samame a wani gida da ke Farakwai a cikin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna inda suka kama wadansu mutane da ake zargin dabi’unsu sun yi kama da na mutanen Maitsine. Malam Usman Yakubu na daya daga cikin wadanda aka kama, sai dai a zantawarsa da Aminiya ya ce su ba wata sabuwar akida suke bi illa su makaranta Al’kur’ani ne. Sannan ya bayyana dalilansu na yin raka’oi hudu a sallar juma’a maimakon biyu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ya sunanka?
Malam Usman Yakubu, kuma uwa daya uba daya nake da shi babban malaminmu. Wanda kuma suna daya muke amfani da shi. Shi ma sunansa ke nan. Mu mutanen Katsina ne, sunan kauyanmu dantsara a yankin Kaita a jahar Katsina.
Aminiya: Yaushe ka zo jahar Kaduna?
Zan samu kusan shekara goma sha biyar , a da muna zaune ne a Birnin Yero kafin daga bisani muka dawo Farakwai.
Aminiya: Me ya taso ku daga Birnin Yero?
Mun baro can ne domin ba mu da kudin yin gini domin haya muke yi a can. Mun yi shekara hudu a Birnin Yero. Yanzu muna cikin shekara na goma ke nan a Farakwai.
Aminiya: Wacce sana’a kuke yi?
Noman doya da abin da ya shafi rogo da masara, sai kiwo da muke yi.
Aminiya: Ta bangaren addini kuma fa wacce kuke yi?
Muna koyar da Alkur’ani ne. Watau mu ‘yan kur’aniyun ne.
Aminiya: Kuna sallah tare da jama’a?
Sai dai idan ba ta kama ba, amma muna sallah tare da jama’a.
Aminiya: Laifin me kuka yi har aka kawo ku wajen ‘’yan sanda?
Sharri ne ya faru na dabbobi shi ne aka kawo mu nan. Akwai yaron da yake wannan guje-guje a gidan,kuma shi shugaban namu ne ya je ya fadi.
Aminiya: A cikin gidan akwai dabbobi da aka samu wadanda aka yanka sannan aka zuba cikin ramuka, naku ne?
Sune dabbobin da aka sato.
Aminiya: Wa ya sato dabbobin?
Tsakani da Allah ban san wanda ya sato su ba, domin ina nan a kulle na samu labarin wai an ga dabbobi da aka yanka a cikin ramuka a gidan, sai na tambayi wadanda muke tsare tare da su cewa ko sun san da dabbobin sai suka ce eh. Ni a gidan nake amma sashe na daban, kuma ina da aure da mata hudu. Ban kuma san inda matan nawa suke ba a yanzu.
Aminiya: Akwai wadansu ramuka a cikin gidan masu zurfi. Na mene ne?
Tun da muka zo Farakwai ba su da wurin sarar kasa haka wanda za ka yi amfani da shi wajen buga bulo domin gini. Ka san kuma harka na makaranta idan aka ce ga malam duk abin da ya ce shi za a yi. Sai ya ba da umurnin mu hako kasa muna yin bulo da shi muna cigaba da gininmu. Duk ramin da ke cikin gidan nan muna hako kasa ne muna amfani da shi wajen yabe da shafe.
Aminiya: Ramin na bullewa ya hade da wani ramin?
A’a bai hade da komai ba. Idan akwai wanda zai yi imani da Allah Ya shiga domin ya gani. Kuma wadannan ramuka a bangaren mai bada karatun akwai rami hudu, ni kuma a sashen gidana daga rijiya sai shadda kawai.
Aminiya: A cikin wadannan ramuka an samu jini da kuma dabbobi da aka yanka a ciki. Wa ya zuba su?
Gaskiya ni ban sani ba, domin ko lokacin da muka je gidan da ‘yan sanda an bincika ramukan amma ba a ga komai ba.
Aminiya: An samu bindiga da harsasai da layu a cikin gidanku. Wa ke da su?
Ita wannan bindiga ba tawa ba ce ta Malam ce, watau Malam Usman mai makarantar. Kuma ni a yanzu ban san inda yake ba.
Aminiya: Ko kuna da alaka da Maitasine?
Ni bakin rayuwata ban san wani Maitatsine ba.
Aminiya: Yaya aka yi aka same ku da katin aiki da hula na soja (ID card) a gidanku?
Wadannan kaya an same su ne a dakin wani Malam Abdullahi, shi ma Almajiri ne, kuma tare muke. Kuma gidansa daban da inda nake. Ita kuma hular soja wani yaro Ali shi ke zuwa kusa da inda sojoji ke aiki, watau Jaji a can ya tsinto.
Aminiya: Shi wannan yaro wanda ya samu kubuta daga gidanku har ya je gidan Mai unguwa ya fadi abin da kuka yi a gidan waye shi?
A’a yaron ma yana dan sace-sace. Duk da ka ganshi dan karami akwai kudaden mutane da yawa a kanshi. Sannan har keke ma ya sato ya ajiye a gidan makwabta.
Aminiya: Batun sallah ya kuke yi?
Muna sallah kamar sauran jama’a, sai dai mu raka’a hudu muke yi a juma’a. Idan kuma Allah Ya sa mun tafi wajen sana’ar mu sai muka tarar ana sallar juma’a za mu iya bi, saboda mun san wadannan hudubobi da liman ke yi biyun nan ita ce aka mayar a cikin hadisi a matsayin raka’a biyu. Sai a karshe a yi raka’a biyu ya tashi raka’a hudu ke nan.
Aminiya: Kuna kabbara kafin sallah?
Eh, mu kan yi kabbara, saboda Allah a cikin Alkur’ani Ya ce wa ManzonSa ka ambaci sunan Ubangijinka ka yi sallah. Idan ka yi bismillah ka fara sallah, sallarka na nan. Idan kuma ka yi ikama kafin ka yi sallah duk sun yi. Dukkansu muna yi ikaman wani lokacin kuma babu ikama. Ga musulmi daya farilla ne, daya kuma sunnah ne.
Aminiya: Me ya sa kuke sallar juma’a raka’a hudu a maimakon biyu?
Idan aka duba cikin Alkur’ani za ka ga inda Allah Ya ambaci sallah Ya ce da safe biyu da magriba raka’a uku. Sannan sallolin rana duk raka’o’i hudu ne. Amma idan aka zo cikin hadisi, juma’a idan aka yi biyun ma babu laifi. Saboda kowa da uzurinsa, wani kuma ba shi da lafiya.
Aminiya: Ko kuna da irin mabiya wannan akida taku a wadansu yankunan jahar nan?
Ka san Barakallahu? akwai mabiyanmu a makarantu a can. Gadar Gayan, ko duk rabin makarantun allo a can duk irin namu ne makaranta Alkur’ani.
Aminiya: Wace akida kuke bi?
Akidar makaranta Alkur’ani, amma wadansu na mana lakabi da ‘yan kala kato, amma mu makaranta Alkur’ani ne kawai.