Ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023 a Jihar Kano, Murtala Sule Garo, ya yi wa ɗaukacin al’ummar Musulmi barka da sallah tare da buƙatar su ɗore da kyawawan halayen da suka koya a Ramadan.
A wani saƙon taya murna, ya ce bikin sallar bai taƙaita ga kammala azumin wajibi na watan Ramadan ba, ya haɗa da faɗakarwa da tunatarwa a tsakanin al’umma don ganin an samu zaman lafiya da arziƙi mai ɗorewa a JIhar Kano da ƙasa baki ɗaya.
- Muna Nadamar Zaɓen Tinubu — Dattawan Arewa
- Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah
“Ina taya ɗaukacin al’ummar Musulmi musamman na Jihar Kano barka da sallah.
“Muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba mu ikon azumtar watan Ramadan. Allah Ya karbi ibadunmu, ya yafe mana kurakuranmu, ya kuma ƙara ara mana lokaci nan gaba.
“Ina kira ga al’umma Musulmi da su yi amfani da darusan da muka koya cikin wannan wata mai alfarma don tabbatar da zama lafiya da ƙaunar juna a jiharmu da kuma ƙasa baki ɗaya.”
Garo, ya ce tabbas ‘yan Najeriya na fuskantar matsin rayuwa sakamakon tabarbarewar tattalin arziki, sai dai ya ce akwai buƙatar a dage da addu’a domin samun sauƙi.
“Tabbas ‘yan Najeriya na cikin wani mawuyacin hali sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziƙi.
“Amma duk da haka ba mu cire ƙauna ga kasarmu ba. Don haka wannan lokaci wata dama ce a gare mu da za mu ci gaba da addu’o’i Allah Ya kawo mana mafita da arziƙi mai ɗorewa.”