Kamfanin sadarwa na MTN ya nemi afuwar aboka hulɗarsa sakamakon matsalar ɗaukewar sabis da kamfanin ya fuskanta a faɗin ƙasar.
To sai dai kamfanin cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce hakan ya faru ne sakamakon yankewar wasu wayoyin sadarwar kamfanin, lamarin ya ya shafi kira da kuma fannin intanet a layin.
- Gwamnati ta yi ƙarin haske kan fargabar rasa ayyuka yayin aiwatar da Rahoton Oronsaye
- An gano haramtattun rukunin gine-gine 68 a Kano
Kamfanin ya kuma ce injiniyoyinsa na aiki domin shawo kan matsalar, inda ya ce sannu a hankali sabis ɗin ya fara dawowa a wasu yankuna.
MTN ya ce an samu yankewar wasu wayoyin sadarwarsa na karkashin kasa tun daga safiya har zuwa tsakar ranar wannan Larabar da suka haɗa da Enugu zuwa Orakam da Umanyare zuwa Mike-Olabayo da kuma hanyar Jebba zuwa Kudu.
Bayanai sun ce tun da tsakar ranar Laraba ne dai masu amfani da layin MTN suka riƙa korafi a sakamakon fuskantar matsalar ɗaukewar sabis a layukansu.