✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MSF ta tura ma’aikatan gaggawa 1,730 Jihar Borno

MSF wanda ake wa lakabi da Likitoci komai da ruwanku sun tura jami’ansu sama da 1,700 zuwa Jihar borno domin bayar da tallafin gaggawa ga…

MSF wanda ake wa lakabi da Likitoci komai da ruwanku sun tura jami’ansu sama da 1,700 zuwa Jihar borno domin bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

Ayyukan jami’an sun hada da bayar da tallafin kula da lafiya, kula da ingancin abinci, da kuma kula da ruwa da tsaftace muhalli.

Shugaban tawagar, Mista Moctar Abassi ne ya sanar da haka ga manema labarai a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli a garin Maiduguri, inda ya ce jami’an sun hada da ‘yan Najeriya 1,600 da kuma ‘yan kasashen waje 130. A cewar Abasi, MSF ta fadada inda take aiki a garuruwa 11, domin samun sauki wajen bayar da tallafi ga wadanda suka bar garuruwansu da marasa galihu na Jihar. Garuruwan da suka amfana da  tallafin sun hada da Maiduguri, Pulka, Gwoza, Monguno, Damask, Benisheik, Dikwa, Banki, Ngala, Rann da kuma Bama.

“MSF na da cibiyoyin kiwon  lafiya 11, wadanda suka hada da bakwai da ake kwantar d marasa lafiya, da kuam tara da ba a kwantar da marasa lafiya. 

A shekarar 2016, kungiyar ta samar da tallafin kiwon lafiya da kula da ingancin abinci ga mutanen da suka bar guruwansu da kuma garuruwan da suka koma,” inji shi.

Abassi ya kara da cewa kungiyar ta bayar da tallafin kiwon lafiya kyauta ga mutane sama da 290,000 wadanda ba a kwantar da su ba, kuma ta duba mata masu juna biyu guda 56,160, inda aka samu mata 5,181 da suka haihu. Haka nan sun bayar da rigakafin ciwon bakon dauro ga yara guda 87,900, sannan kuma sun raba sama da tan 1,099.2 na abinci a karkashin shirin bayar da tallafin abinci na kungiyar.

Da yake jawabi a kan samar da ruwan sha da tsaftace muhalli kuwa, shugaban na MSF cewa ya yi sun gina makewayi guda 282, da tankunan ruwa 38 da kuma famfon tuka-tuka  87 a garuruwan da rikici ya shafa.