✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Motar yashi ta muttsuke mutum 6 a Adamawa

Mota makare da yashi ta kwace, ta auka garejin gyaran motoci inda ta kashe mutum shida

Wata babbar motar yashi ta muttsuke mutum shida har lahira, ciki har da wani mai ba da hannu a garin Yola, Jihar Adamawa.

Lamarin ya faru ne bayan motar, makare da yashi ta kwace, ta yi cikin wani garejin gyaran motoci, inda ta yi ajalin mutanen.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa, “Tifar da ke dauke da yashi a lokacin ta kwace ne sannan ta kade mutanen a garejin kanikawa.

“Direban tifar ya tsere, amma mutane sun kona motar.”

Shi ma wani ganau, Yakubu Ayuba, ya ce, wutar da fusatattun matasa suka banka wa motar ta yadu ta koma wasu shaguna da ke wurin da abin ya faru.

Yakubu Ayuba ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne a unguwar Vinukilang da ke wajen garin Yola.

Jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) da ’yan kungiyar agaji ta Red Cross ne suka kwashe gawarwakin daga wajen.