✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Motar siminti ta muttsuke mutum 3 har lahira

Mutum uku sun rasu, wasu biyu sun jikkata, bayan wata babbar mota makare da siminti ta kwace afka kan wani shago.

Mutum uku sun rasu, wasu biyu sun jikkata, bayan wata babbar mota makare da siminti ta afka kan wani shago.

Motar simintin da ke tafiya a guje, ta kwace ta yi cikin shagon ne, inda ta danne mutanen a kan babban titin Legas-Abeokuta dsa ke Jihar Ogun a ranar Talata.

Kakakin Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da aukuwar hatsarin, wanda ta ce ya ritsa kuma da wani mai babur.

Ta danganta hatsarin da “gudun wuce misali da kuma tsinkewar burkin babbar motar ta da taho daga yankin Sango za ta je Legas.

“A lokacin da motar take saukowa daga gangara ne burkinta ya tsinke, ta sauka daga hanya ta auka cikin shagon,” in ji ta.

Ta bayyana cewa an garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa Babban Asinin Otta, inda aka ajiye gawarwarkin a mutuwari.