✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Motar kwashe ’yan Najeriya ta yi gobara a hanyar Port Sudan

Daya daga cikin motocin da suka kwashe ’yan Najeriya daga Khartoum, ta kama da wuta a hanyarta ta kai su Port Sudan

Daya daga cikin motocin da suka kwashe ’yan Najeriya daga Khartoum, babban birnin kasar Sudan, ta kama da wuta a hanyarta ta kai su Port Sudan a safiyar Litinin.

A daren Lahadi motoci 26 dauke da ’yan Najeriya da suka makale a Sudan bayan barkewar yaki suka bat Jami’ar Al Razi zuwa Port Sudan.

“Da misalin karfe 2.30 na dare wata ta kama da wuta daga cikin wadanda suka kwashi ’yan Najeriya za su kai su Port Sudan.

“Motar, mai alamar Jihar Katsina na dauke da mace daya da maza 49, ta kama da wuta ne bayan direban ya tsaya a kusa da shingen binciken mayakan RSF, sakamakon tsananin zafi da ya sa tayarta kamawa da wuta kafin ta yi bindiga.

“Bayan lalacewar motar, wadda Shugaban Kungiyar Dattawan ’Yan Najeriya, Dr Hashim Idris Na’Allah, ke ciki, an sanya wasu fasinjojin a cikin sauran.

“Sauran kuma a wurin suka kwana tare da direban da mayakan RSF, kafin washegari su kama hanya.

“Sun bayyana cewa mayakan sun yi ta fadi-tsahin ganin an gyara motar, har suka ba su shayi” in ji Sani Aliyu da ke Sudan.

Tuni dai ’yan Najeriyan suka ci ga da tafiya a motar tasu zuwa Port Sudan inda ake sa ran za su tsallaka zuwa kasar Saudiyya, daga can a kwaso su zuwa gida.

Sama da ’yan Najeriya 1,500 ne suka tafi Port Sudan bayan rukunin farko sun kwana hudu ba tare da sun samu izinin kasa tsallakawa zuwa kasar Masar, inda jirage ke jiran su domin dawo da su gida ba.

Daga baya dai Shugaba Buhari ya sa baki, hukumomin Masar sun ba su damar shiga kasarsu.