Wata motar sintiri ta Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta yi hatsari inda ta kashe mutum biyu ta kuma jikkata wasu biyar a babbar tashar motar Alkaleri a Jihar Bauchi.
Motar dai ta kwace wa direbanta ne sannan ta tunkari wani shagon da ke cikin tashar, wacce ke kan babbar hanyar Bauchi zuwa Gombe, har ta kashe mutanen.
- Najeriya A Yau: Zeben Gwamna: Mutanen Anambra Sun Ba Da Mamaki
- Maciji ya sare shi a hanya bayan ya gudo daga hannun masu garkuwa da shi
Kwamandan shiyya na hukumar a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ne ya tabbatar da hatsarin ga manema labarai ranar Lahadi a Bauchi.
Ya ce, “Jami’anmu na kan hanyar dawowa ofis daga sintirin da suka saba yi , kwatsam sai direban ya kwalla ihu bayan ya fita daga hayyacinsa, motar ta kwace masa ya sauka daga hanya gaba daya.
“A sakamakon haka, motar ta fada kan wasu mutane da ke tsaye a bakin wani shago, inda ta danne mutum 14, ciki har da manya 10 da kananan yara hudu.
“Kowa zai iya samun rashin lafiya a kodayaushe. Har yanzu ma direban bai san a halin da yake ciki ba, yana Babban Asibitin Alkaleri,” inji Kwamandan.
Daga nan sai ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah ya jikansu, inda su kuma wadanda suka jikkata ya yi addu’ar samun sauki a gare su.
Tuni dai aka ajiye gawarwakin mutanen a dakin adana gawarwaki, yayin da wadanda suka jikkata kuma suke can suna samun kulawa.