Daya daga cikin motocin dakon kaya mallakin Kamfanin Dangote, ta kashe yara uku tare da jikkata iyayensu a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na dare yayin da duk mazauna suke sharar barci.
- Dalilin dawo da hoton Sanusi a dakin taron gidan gwamnatin Kano
- An maka Sarkin Dutse a gaban kotu kan rabon gadon mahaifinsa
Ya bayyana cewa, motar ce ta kwace wa direban kuma ta rusa gidan wani mutum mai suna Mallam Abdu Zailani, har uwar daki inda ta danne yaran suna tsakar barci.
Hakan ce ta yi sanadiyyar mutuwar yaran uku tare da jikkatar iyayensu da a yanzu an kwantar da su a asibiti.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a gida mai lamba 162 a Unguwar Juma da ke Zariya.
Aminiya ta samu cewa, ainihin direban motar Mallam Abdullahi, ba shi da masaniyar lokacin da karen motar mai shekaru ya dauki mukullin motar ya tafi yawo da wasu abokansa.
Jami’in dan sanda mai kula da shiyyar Zariya, DPO Kasim Abdul ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kazalika, ya ce tuni sun cika hannu da direban motar wanda ake ci gaba da gudanar da bincike a kansa.
Sarkin Fadar Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika wanda makoci ne ga magidancin da lamarin ya rutsa da shi, ya ce za a yi duk mai yiwuwa domin ganin shari’a ta yi aiki.