✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Dangote ya ba da tallafin naira biliyan 1.5 a Maiduguri

Ba kowane mai kuɗi ba ne yake da zuciyar bayarwa.

Hamshaƙin attajirin Afirka, Aliko Dangote ya bayar da tallafin naira biliyan ɗaya da rabi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a birnin Maiduguri na Jihar Borno.

Dangote ya ce ya bayar da naira biliyan ɗaya ga hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya, NEMA, da kuma naira miliyan 500 ga gwamnatin Jihar Borno.

Attajirin ya bayyana hakan ne yayin ziyarar jaje da ya kai Maiduguri tare da Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasawara a ranar Juma’a.

Shi ma Gwamna Sule ya sanar da bayar da tallafin kayayyakin jin kai domin rage raɗaɗin waɗanda ambaliyar ruwan ta shafa.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi jinjina a gare su dangane da wannan gagarumar kyauta da soyayyarsu ga mutanen Borno.

“Ba kowane mai kuɗi ba ne yake da zuciyar bayarwa. Kuma wannan ba shi ne karon farko da Aliko Dangote yake taimakon mutanenmu ba.

“Ina rokon Allah Ya saka masa da gidan Aljannah,” a cewar Gwamna Zulum.

“Ina kuma miƙa godiya ga ɗan uwana, Gwamna Abdullahi Sule da ya zo jajanta mana tare da Dangote.”