✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan NNPC ba ɓarayi ba ne — Kyari

NNPC ba zai yi wa 'yan ƙasa ƙarya ba. Mu ba masu laifi ba ne kuma ba ɓarayi ba ne.

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya yi watsi da zargin cewa ma’aikatan kamfanin na da hannu wajen shigo da man fetur marasa inganci a ƙasar.

Ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Laraba lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar dattawa kan zargin zagon ƙasa a harkar man fetur.

Kyari ya ce a matsayinsa na babban jami’in kamfanin NNPCPL, ya fuskanci ƙalubalen da bai dace ba daga kafafen yaɗa labarai da kuma mutanen da ke zargin cewa kamfanin yana aikata abin da zai haifar wa tattalin arzikin ƙasar zagon ƙasa.

“Kamfanin mai NNPCL bai aminci ba kuma ba zai yi wa ƙasa ƙarya ba.

“Mu ba masu laifi ba ne kuma ba ɓarayi ba ne. Za mu kare mutuncinmu domin mu yi wa ƙasar nan hidima,” in ji shi.

Da yake yin ƙarin haske, ya bayyana cewa masana’antar mai da iskar gas na cikin wani yanayi, yana mai cewa akwai abubuwan da suka sani amma ba za su iya magana a fili ba har sai lokacin ya zo.

Wannan dai ya biyo bayan cece-kucen da aka samu a bayan nan dangane da kamfanin da kuma yanayin ayyukansa.

Da yake jawabi a zauren Majalisar Wakilai a watan Yuli, Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce rahotanni sun nuna cewa wasu ma’aikatan NNPC, da dillalan man fetur da kuma tashoshi sun buɗe wata masana’anta a Malta.