Garambawul din da kungiyoyi suke yi a kokarin kauce wa fadawa cikin matsaloli dalilin cutar coronavirus da ma wasu matsalolin kudi sun sa Moses da Ighalo da Lacazette cikin halin tsaka mai wuya inda Neymar zai ci gaba da zama a kungiyar PSG.
Ko me ya sa?
Moses ya shiga tsaka mai wuya
Dan wasan gaban na Najeriya wanda Chelsea ta tura aro zuwa kungiyar Inter Milan, Victor Moses, ya shiga halin tsaka mai wuya ne bayan da ya kaza tabuka abin a zo a gani a Italiya.
A wasanni bakwai da ya buga tun zuwansa kungiyar ta birnin Milan, Moses bai burge hukumomi da ma magoya bayan kungiyar ba inda ya yi ta fama da rashin lafiya.
- Traore, Vertonghen da Diaby na shirin sauya sheka; Chelsea na neman dan wasan Barca
- Juventus na shirin gwanjon Pjanic, Costa da Higuain
Kungiyar Inter Milan ta nemi sayen dan wasan; Chelsea ta bukaci Euro miliyan 10 amma Inter ta yi tayin dan wasan a kan Euro miliyan shida.
Kwantiraginsa a Chelsea zai kawo karshe a karshen kakar 2021, amma babu alamar kocin Chelsea din, Frank Lampard, yana da shirin dawo da shi.
Zawarcin Werner ya sa Liverpool sayar da ‘yan wasa uku
Duk da nasarorin da take samu da haskawa da take yi a gasar Premier, kungiyar Liverpool tana nazarin dauko dan wasan gaba na kungiyar RB Liepzig, Timo Werner.
Hakan dai ya sa a daya bangaren take shirin sallamar ‘yan wasanta uku wadanda zuwa yanzu ba a bayyana sunayensu ba.
Jaridar wasanni ta Athletic a Spaniya ta ce Liverpool za ta siyar da ‘yan wasan ne saboda biyan kudin dauko dan wasan wanda farashinsa ya kai Euro miliyan 52.
Dawowar Rashford na yi wa Ighalo barazana a United
Matashin dan wasan kungiyar Manchester United, Marcus Rashford, wanda ya kwashe watanni yana jinya ya murmure kuma zai dawo wasa.
Hakan ya kawo rashin tabbas a ci gaba da kasancewar dan wasan Najeriya Odion Ighalo, wanda kungiyar ta dauko aro saboda ya cike gibin da rashin Rashford ya samar.
Jaridar Skysport ta rawaito cewa dawowar Rashford din za ta sa United ta sake duba kwantiragin aro da ta yi na dauko Ighalo daga kungiyar Shanghai Shenhua.
Arsenal za ta ba da Lacazette saboda Lemar
Kungiyoyin Arsenal da Atletico Madrid suna shirin rattaba hannu a kan wata yarjejeniya da za ta bai wa Arsenal damar dauko Thomas Lemar daga Atletico din idan ta ba da dan wasan gabanta Alexandre Lacazette.
Jaridar wasanni ta AS ta ce Lemar din, wanda ya kwashe shekara daya bai ci kwallo ba, yana iya kara kaimi wa tsaron bayan Arsenal din.
Coronavirus ta sa Neymar zai ci gaba da zama a PSG
Tasirin da coronavirus ta yi a kan kungiyar Barcelona, wadda ke kokarin dawo da dan wasan zuwa Camp Nou, zai sa Neymar ya ci gaba da zama a PSG.
Neymar da Barcelona dai sun raba gari ne lokacin da PSG din ta sayo Neymar a matsayin dan wasan da ya fi kowa tsada a duniya a kan Euro miliyan 222.
Jaridar Daily Star ta bayyana cewa tun bayan tafiyar Neymar din ne dai Barcelona take bibiyar dan wasan tana kokarin shawo kansa ya dawo kungiyar.
Hakan zai fuskanci koma baya dalilin tasirin da cutar Coronavirus ta yi a kan lalitar kungiyar ta Barcelona.