Tawagar kwallon kafar Morocco ta samu gagarumar nasara akan Belgium a Gasar Kofin Duniya da ke gudana a Qatar, inda ta doke ta da ci 2-0 a karawar da suka yi a Lahadin nan.
Abdelhamid Sebri ya jefa wa Morocco kwallon ta na farko a minti 73 da fara wasan, yayin da zakaria Aboukklal ya jefa kwallo ta biyu a minti 93.
- Shugaban da ya shafe shekara 43 a karaga ya sake lashe zabe
- An rufe makarantu 50 kan magudin jarrabawa a Oyo
Wadannan kwallaye biyu sun bai wa kasar nasara da kuma hawa teburin rukuni na 6 da maki 4, yayin da Belgium ta koma matsayi na biyu da maki 3.
Wannan gagarumar nasara ta faranta wa ’yan Afirka rai, lura da cewar har yanzu kasashen da ke wakiltar nahiyyar basu samu nasara ba, baya ga nasarar Senegal.
Haka kuma, ’yan Afirkan sun yi murna lura da cewa Belgium ce ke mataki na 4 a kasashen da suka fi iya kwallo a duniya.
Yanzu haka ana karawa tsakanin Croatia da Canada wadanda suma suke cikin wannan rukuni na gasar, yayin da Croatia ke da maki guda, ita kuwa Canada ba ta da maki.
A karawar da aka yi da safe, Costa Rica ta doke Japan da ci 1-0, yayin da anjima da karfe 8 Spain za ta fafata da Jamus.