✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Misis Lydia Isaac-Nagu : A matsayina na lauya ’yar Arewa na fuskanci kalubale a Kudu – Lydia

Misis Lydia Isaac-Nagu lauya ce da ta shafe fiye da shekaru 24 ta na aikin lauya. Lydia ’yar asalin karamar Hukumar Wukari ce ta jJhar…

Misis Lydia Isaac-Nagu Misis Lydia Isaac-Nagu lauya ce da ta shafe fiye da shekaru 24 ta na aikin lauya. Lydia ’yar asalin karamar Hukumar Wukari ce ta jJhar Taraba. Ta bude ofishinta a yankin Ikeja da ke jihar Legas inda ta sanya masa suna Amachum Chambers. Misis Lidiya ta bayyana irin gwagwarmar da ta sha a matsayinta na lauya mace da ke aiki tare da maza da kuma kalubalen da ta fuskanta a matsayinta na ’yar Arewa da ke aikin lauya a yankin Kudu. Ga yadda hirar ta kasance:
Tarihi
Sunana Misis Lydia Isaac-Nagu ni lauya ce sunan kamfanina Lydia Isaac-Nagu and Associate a karkashin Amachum Chambers  da ke yankin Ikeja a Jihar Legas. An haife ni a karamar hukumar Wukari. Na fara makarantar firamare a Ibiniza Primary School  da ke Wukari Goberment Girls School a garin Yola da ke tsohuwar Jihar Gongola, na kuma kammala a shekarar , daga nan na samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda na karanta fannin lauya a tsangayar harkokin Shari’a da ke Kongo. Na gama karatuna a shekarar 1988 daga nan sai na taho Jihar Legas domin yin karatun lauya, inda na kammala cikin nasara. Daga bisani na yi hidimar kasa a ma’aikatar shari’a ta Jihar Legas. Na fara aikin lauya a ofishin fitaccen lauyan nan mai suna Benga da ke yankin Ikeja a matsayin karamar lauya. Na auri mijina Injiniya Isaac Nagu. Daga nan aka yi masa sauyin wurin aiki zuwa garin Warri. Muka tafi gaba daya, inda muka yi shekara hudu a can. A can ma na yi aiki da wani ofishin fitaccen lauya da ke unguwar Hausawa a matsayin karamar lauya. Da aka dawo da shi Legas, sai na biyo shi muka dawo tare. A nan na bude ofishina a shekarar 1992. Na fara ni kadai a matsayin shugabar ofishin, tare da wasu kananan lauyoyi.
Abin da ya ba ni sha’awa na zabi na karanta fannin aikin lauya
Gaskiya ni tun ina ’yar karama nake burin na zama lauya saboda yadda nake karantawa a jarida irin yadda lauyoyi ke yin aiki. Kuma ni Allah ya ba ni fasahar iya magana, domin tun ina karama mutane suke cewa lallai zan zama lauya, domin na iya magana, amma shi mahaifina a lokacin ba ya son aikin lauya saboda yadda ake cewa lauyoyi ba za su shiga aljanna ba. To shi kuma ba ya so mu kasance cikin irin wadannan lauyoyin. A lokacin sai ya rika tambayar mutane har aka fahimtar da shi cewa aikin lauya yana da kyau idan mutum zai yi bisa tsari da doka, tare da gaskiya da rikon amana. Daga bisani sai ya yarda.
Yadda muka hadu da mijina
Mun hadu da shi tun muna yara. Shi ma Bajukune ne daga garin Wukari a Jihar Taraba. Haka muka rika soyayya, har  ya tafi Turai karatu ni ma na yi nawa karatun a nan gida Najeriya.Bayan mun gama sai muka yi aure. Yanzu muna da ’ya’ya uku. Babbar ’yarmu ta kammala karatunta a halin yanzu ta na aiki da kamfanin jiragen sama na Dana Airline. bisani na dawo Legas.
Abin da na fi sha’awa idan na tashi daga ofis na koma gida
Bayan aikin ofis na fi sha’awar na shiga cikin kicin na dafa abinci na yarana da na maigidana. Kuma na fi sha’awar na ci tuwo saboda mu ’yan Arewa mun fi son tuwo.Ban da launin baki da fari na kayan aikina na fi son launin shudi.
Wuraren da na ziyarta
Na je kasar Birtaniya, inda na sauka a birnin Ingila, kuma har sau biyu na je kasar Gana da Togo da sauran kasashen Afirka da yawa. Amma yanzu na fi son na je Amurka, duk da haka na fi son kasa ta Najeriya domin ni ’yar Najeriya ce, kuma ina alfahari da kasancewa ta ’yar Arewa.
Abin da ya fi damuna
Babbban abin da yake damuna shi ne rashin zaman lafiya da yake faruwa, musamman a yankin Arewa. Da cin hanci da rashawa da kabilanci da bambancin addini da talauci da koma-bayan tattalin arziki. Kuma ni ina dora alhakin wadannan matsaloli a kan ’yan siyasa. Ya kamata mu gyara.
 Shawarata ga mata
Shawarar da zan bayar ita ce matanmu su karanta fannin lauya, saboda akwai amfani da albarka a ciki. Kuma mutane za su rika girmama ka. Kuma ina ba su shawarar cewa idan suka karanta fannin lauya su yi kokari su yi aikin lauya, kada su tsaya a aikin gwamnati domin yadda abubuwan suke tafiya, nan gaba aikin gwamnati zai zama ya yi karanci. Kamata ya yi kowace mace da ta samu kanta a tsakanin maza ta mayar da hankali kan aikinta kada ta bari wani abu ya karya mata gwiwa kuma ta dage da addu’a.

Dalilin da ya sa ba na yin siyasa
Gaskiya ba na siyasa saboda ba na sha’awar ta, musamman saboda irin yadda ’yan siyasa suke gudanar da al’amuransu. Shi ya sa na fi sha’awar na mayar da hankali kan aikina na lauya, har na cimma burin da na sa a gaba. Kuma ba ni da wata kungiya mai zaman kanta sai dai nakan shiga al’amuran  kungiyar mata lauyoyi. Ba na so na shiga wani abu da zai dauke min hankalina daga aikina na lauya shi ya sa ka ga ba na damun kaina da shiga cikin kungiyoyi.
 kalubalen da na fuskanta a matsayina na lauya mace
Babu shakka aikin lauya a matsayina na mace a cikin maza na tattare da kalubale masu yawa. Domin za ka ga mutane suna daukar cewa namiji zai fi mace yin abinda ya kamata. Suna ganin cewa mata muna da matsalolin gida da na iyali wanda suke ganin zai hana mu tsayawa kan aiki, amma kuma abin ba haka yake ba. Musamman mu mutanen Arewa da ba ma barin matanmu su fita aiki. Amma na gode wa Allah maigidana mutum ne mai hakuri da juriya, wanda ya fahimci yanayin aikina. Ya ba ni goyon baya dari bisa dari. Kamar a Jihar Legas da dama a nan suna yi wa ’yan Arewa kallon raini cewa ba za mu iya aikin lauya ba. Na sha wahala kwarai da gaske kafin na samu shiga a wurin mutanen gari da lauyoyi ’yan uwana. Akwai kalubalen rashin fahimtar aikin lauya daga mutanenmu ’yan Arewa da ke zaune a Jihar Legas, domin shi mutumin Arewa ba ya son zuwa kotu duk abin da ya faru a gare shi yakan bar wa Allah komai.
Dalilin da ya sa na fi karkata ga bangaren harkokin kadara a  maimakon zuwa kotu yin shari’a.
Da na lura cewa aikin lauya na bangaren zuwa yin shari’a a kotu ya na da damuwa, sai na karkata akalar aikina zuwa bangaren lura da kadarorin jama’a da saya da sayar da kadarori da bude kamfanoni ga jama’a. Wannan bangare ya fi kwanciyar hankali, domin shi ba kodayaushe ake zuwa kotu ba, sai in an samu matsala. Wani lokaci za ka iya yin shari’a na tsawon shekaru ba tare da ka samu biyan bukata ba. Yau shekarata kimanin 15 ina wannan bangare.
Nasarorin da na samu
Na samu nasarori da yawa fiye da shekara 24 da na yi ina aiki lauya. Yanzu haka na yi suna a yankin Kudu. Na zama lauya wacce ta yi fice a tsakanin alkalai da lauyoyi da yawa. Na sami ci gaba dangane da harkar kadarori, wadanda nake saya na sayar.Kuma ina burin na cimma abubuwa da yawa har na zama babbar lauya mai rike da mukamin SAN. Ina burin na rika taimakon jama’a a nan gaba na kafa kungiyar taimakon talakawa da marayu da mata.
Abin da ba zan taba mantawa ba a aikina na lauya
Akwai abubuwa da yawa da suka faru amma wanda ba zan manta da shi ba shi ne lokacin da nake garin Warri akwai lokacin da nake yin wata shari’a da har sai da na yi kuka. Wato matsalar gado ce. Wata mata ce ta kawo min koken cewa maigidansu ya auri mata uku sai ya mutu. Da ya mutu sai aka ce ba za a ba danta da ta haifa da shi gado ba, saboda mutumin bai biya sadakinta ba. To mahaifiyar mutumin  tsohuwa ce tukuf da za ta ba da shaida mu yi nasara a shari’ar, mun  dauko ta zuwa kotu, amma sai alkali ya ce ba zai saurari kararmu a ranar ba. Saboda haka sai na fashe da kuka saboda tausayin tsohuwar da irin wahalar da ta sha. A karshe tsohuwar mutuwa ta yi ba tare da ta ba da shaida ba. Na yi bakin cikin kwarai da gaske.Daga