Misis Ann Dogonyaro ita ce Shugabar Matan Jam’iyyar APC ta Jihar Nasarawa, kafin wannan matsayi malamar lafiya ce a Asibitin Ma’aikata da ke Akwanga a Jihar Nasarawa. A shekarar 1998 ta zama Kodinetar kungiyar taimaka wa mata ta Najeriya, kungiyar da Maryam Sani Abaca ta kirkiro don taimaka wa mata har ma da karuwai don su dogara da kansu. A hirarta da Zinariya ta bukaci mata su kama sana’a, zawarawa kuma su tsare mutuncinsu.
Tarihin rayuwata
Sunana Misis Ann Dogonyaro. An haife ni a Kogon Rafi a Jihar Kaduna. Na yi firamare a Kogon Rafi daga 1970 zuwa 1976. Bayan na kammala sai na koma wurin kawuna da ke garin Jos a Jihar Filato. A wurinsa na ci gaba da karatu inda ya sanya ni a makarantar sakandare ta Commercial Secondary School. Daga nan sai makarantar School of Health and Technology da ke Pankshin duk a Jihar Filato, wato daga 1979 zuwa 1980. Bayan na kammla sai na fara aiki a asibitin sha-ka-tafi na garin Jos. Bayan an kirkiro karamar Hukumar Jos ta Kudu ne sai fara koma aiki da Kwalejin Koyon Sana’oi (Gobernment Technical College) a matsayin daya daga cikin malaman lafiyar kwalejin. Daga nan na sake koma wa Jami’ar Jos a shekarar 1995 na yi digiri.
Bayan na kammala karatun digiri sai na sake koma wa karamar Hukumar Jos ta Kudu na ci gaba da aikina. Bayan an kirkiro Jihar Nasarawa a 1996 sai a shekarar 1997 na dawo karamar Hukumar Akwanga, sannan na fara aiki a asibitin ma’aikata. A shekarar 1998 na koma Abuja bayan na zama Kodinetar kungiyar National Council of Women Society Of Nigeria. Maryam Sani Abaca ce ta kirkiro wannan kungiyar da nufin a taimaka wa mata har ma da karuwai don su dogara da kansu, maimakon dogara ga mazajensu kawai.
A bangaren siyasa kuwa, na fara ne a tsohuwar jam’iyyar AD kafin daga baya ta koma jam’iyyar AC, inda na rike mukamin shugabar matan jam’iyyar ta Jihar Nasarawa. Daga nan muka ta sake komawa jam’iyyar ACN a nan na ci gaba da rike mukamina. Daga baya sai aka daukaka matsayina zuwa mataimakiyar shugaban jam’iyyar ACN ta Jihar Nasarawa. Matsayin da nake rike da shi ke nan har aka hade aka kafa jam’iyyar APC, inda aka ba ni mukamin shugaban matan jam’iyyar Jihar nan.
Halayen da na koya a wurin iyaye
Ina yi wa iyayena godiya ta musamman dangane da kyakkyawar tarbiya da suka yi mini, domin ita ce ta kai ni matsayin da nake a yau. Iyayena sun ce kada na yi karya; sun ce duk halin rashi da zan shiga kada na yi sata, ba su kuma koya mini kin jama’a ba. Mahaifina mutum ne mai son jama’a, ya kuma koya mana haka. Misali idan ka je kauyenmu za ka ga Fulani birjik, to duk mahaifina ne ya ba su filaye kyauta suka yi gini. Saboda haka dukkanmu a gidanmu mun saba da jama’a sosai, musamman ni idan aka je gidana za a ga ina tare da jama’a da dama, ina taimaka musu daidai gwargwado. Haka ma a wajen aikina za a ga ina tare da jama’a a kowane lokaci. Iyayenmu sun yi mana kyakkyawar tarbiyya da muke amfana da ita sosai a rayuwarmu ta yau-da-kullum. Hakan ya sa nake kara amfani da wannan Zinariya wurin sake gode musu.
Nasarori
Kamar yadda na bayyana a lokacin da nake ba da tarihina, tabbas na samu nasarori da dama a rayuwata. Amma babbar nasara a wurina wadda nake alfahari da ita a yau ita ce, wadda na samu a lokacin da nake aiki da kungiyar National Council Of Women Society of Nigeria. A gaskiya ba wai yabon kai ba mun taimaka wa mata da kuma karuwai wajen kawo kyakkyawan canji a rayuwarsu. Mun ba su shawarwari, mun taimaka musu da kudin da suka fara sana’oin da suka ba su damar dogara da kansu. Haka su ma karuwai, da yawansu sun daina harkar karuwanci, sun kama sana’oi sanadiyar kyawawan shawarwari da kuma tallafin da muka ba su. Shi ya sa a koyaushe nake alfahari da haka. Haka ya sa nake kira a daina kyamar karuwai, idan aka ja su a jiki sai a ba su shawarwari da tallafin da za su gyaru, su kuma taimaki wasu.
kalubale
Ba a rasa kalubale a rayuwa. Na fuskanci kalubale da dama a bangaren iyalina da siyasa da kuma aikina. Bari in fara da bangaren siyasa: idan kana so ka yi gyara sai ka ga wasu mutane ba sa son haka, don ba su fahimci manufarka ba. Dole sai ka fahimtar da su sosai kafin su fahimci abin da kake nufi. Idan ba haka ka yi ba to, babu shakka za ka ji sun shiga gari suna zagin ka. Wannan shi ne babban kalubalen da nake fuskanta a shugabancin matan jam’iyya a bangaren siyasa.
A bangaren iyalina: Maigidana ya dade da mutuwa (Allah Ya gafarta masa). Ya rasu ya bar ni da ‘ya’ya 4, duka maza. Tun daga lokacin ni kadai nake daukar nauyin komai game da rayuwarsu. Iliminsu da abin da za su ci na yau da kullum da dai sauransu duk ni nake yi. Kowa ya sani wannan ba karamin nauyi ba ne, kuma ya zama mini babban kalubale. Amma na gode wa Allah kasancewar duk da haka ban taba zuwa wurin wani ko wata ina neman taimako ba. Allah Yana tanadar mini da duk abubuwan da suke bukata a rayuwarsu har zuwa yanzu.
Burina
Babban burina a rayuwa kullum shi ne in ga ina taimaka wa jama’a musamman nakasassu. Kamar yadda na yi bayani a baya na fito ne daga gidan taimako. Ma’ana mahaifina ya koya mana halin taimaka wa jama’a musamman marasa galihu. Saboda haka idan gari ya waye har dare ya yi ban kuma yi wa wani mutum abin da zai je dadi ba sai na ji bakin ciki ya lullube ni. Amma da zarar na aikata alheri sai in ji ina cike da farin ciki.
Shawarata ga mata
Mata sun kasu kashi uku, wadanda suka yi aure da ‘yan mata da kuma wadanda mazajensu suka mutu. Ga matan aure, shawarar da zan ba su ita ce su rika mazajensu hannu bibbiyu, domin ba za su san amfaninsu ba sai sun rasa su. Su rika yi wa mazajensu godiya a duk lokacin da ya ba su wani abu, ko kuma ya kawo wani abu gida, idan babu su yi hakuri. Kuma mata su daina dogara da mazajensu, su kama sana’a. Wadannan su ne irin halayen da na koya a wurin matar tsohon marigayi shugaban kasa Maryam Sani Abaca.
Ga matan da mazajensu suka rasu kuma wadda ni ma ina cikinsu, shawarata gare mu ita ce, duk da cewa muna fuskantar matsalolin rayuwa da dama amma Allah Yana tare da mu a kullum. Mu ci gaba da yin hakuri, kada mu zubar da mutuncinmu da kuma darajarmu wai don mazajenmu sun mutu. Mu tuna fa muna da ‘ya’ya don haka ya zama wajibi mu lura da su don wannan babban hakki ne a wuyanmu.
Ga ‘yan mata kuma su guji kwadayi da kyale-kyalen duniya, su tsaya tsayin daka don ganin sun auri miji nagari, kada su damu da dukiya.