✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministocin Tinubu: El-Rufai, Wike, Badaru sun samu shiga

Tsofaffin gwamnonin jihohin Kaduna, Rivers da Jigawa sun samu shiga cikin jerin sunayen  da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa domin tantancewa…

Tsofaffin gwamnonin jihohin Kaduna, Rivers da Jigawa sun samu shiga cikin jerin sunayen  da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa domin tantancewa a matsayin ministoci.

A ranar Alhamis shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana sunaye 28 da suka fito a kashin farko na mutanen da za a tantance domin naɗa su muƙamin minista.

Sunayen sun haɗa da Nasiru El-Rufa’i, Nyesom Wike, Badaru Abubakar, Ahmed Ɗangiwa, Hannatu Musawa, Uche Nnaji, Betta Edu da Doris Aniche Uzoka.

Akwai kuma David Umahi, Ekperipe Ekpo, Nkiru Onyeojiocha, Olubunmi Tunji Ojo, Stella Okotette, Uju Kennedy Ohanenye, da Bello Muhammad.

Sai kuma Dele Alake, Lateef Fagbemi, Muhammad Idris, Olawale Edun, Waheeb Adabayo Adelabu, Iman Suleiman Ibrahim, Ali Pate, Joseph, Abubakyar Kyari, John Eno, da Sani Abubakar Ɗanladi.