Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kai wata ziyara sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa da ke Abuja, a ranar Laraba.
Ziyarar dai kawo yanzu babu wanda ya san gaskiyar dalilin ta.
SDP na daga cikin jam’iyyun da suka shiga zaben 2023, wanda El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa a cikin jami’yyar APC da ta yi nasara a jiharsa ta Kaduna da kuma matakin Shugaban Kasa.
Sunan Malam Nasiru na daga cikin wadanda aka mika wa majalisa domin tantnacewa a matsayin minista, sai dai bai samu sahalewar majalisar ba, sakamakon wasu dalilai da har yanzu ba a bayyana ba.
- An gurfanar da Amal kan zargin bai wa dan sanda cin hanci
- Majalisa ta amince da ƙudirin yi wa Alƙalai ƙarin albashi
Bayan wannan tirka-tirkace El-Rufa’i ya yi batan dabo a siyasa, inda ba a kara jin duriyarsa ba a siyasance sai wannan ziyara da ya kai ofishin jam’iyyar SDP.
Ziyarar tasa ta soma yamutsa hazo, inda wasu ke alakanta ta da siyasar 2027.