✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ministoci 9 sun halarci zaman Majalisar Zartarwa

A yanzu haka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar zaman Majalisar Zartarwa a fadar gwamnatinsa ta Aso Villa da ke babban birnin Tarayya Abuja. Wannan…

A yanzu haka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar zaman Majalisar Zartarwa a fadar gwamnatinsa ta Aso Villa da ke babban birnin Tarayya Abuja.

Wannan shine zaman majalisar na 26 da Shugaban Kasar yake jagoranta ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna inda ake amfani da intanet.

Zaman majalisar ya fara gudana da misalin karfe 10.00 na safiyar Laraba, 25 ga watan Nuwamban 2020.

Manyan ’yan majalisar da suka halarci zaman a wannan mako sun hadar da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha;  Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da Mai ba da Shawara kan Harkokin tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno.

Ministoci 9 ne suka albarkaci zaman da suka hada da; Ministan Kudi, Kasafi da Tsare-Tsaren – Zainab Ahmed; Ministan Ruwa – Suleiman Adamu; Ministan Labarai da Al’adu – Alhaji Lai Mohammed.

Sauran sun hadar da; Ministan Ayyuka da Gidaje – Babatunde Fashola; Ministan Matasa da Wasanni – Sunday Dare; Ministan Harkokin Cikin Gida – Ogbeni Rauf Aregbesola.

Sai kuma Ministan Lantarki – Sale Mamman; Ministan Harkokin Waje – Geoffery Onyeama da kuma Ministan Noma – Sabo Nanono.