A yanzu haka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar zaman Majalisar Zartarwa a fadar gwamnatinsa ta Aso Villa da ke babban birnin Tarayya Abuja.
Wannan shine zaman majalisar na 26 da Shugaban Kasar yake jagoranta ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna inda ake amfani da intanet.
- Buhari ya gaza, ba ta mu yake ba —Yankin Arewa
- An dawo da kayan tallafin COVID-19 da aka yi warwaso a Filato
- Tsaro: Buhari ya manta da rantsuwarsa da Al-Qur’ani — ACF
Zaman majalisar ya fara gudana da misalin karfe 10.00 na safiyar Laraba, 25 ga watan Nuwamban 2020.
Manyan ’yan majalisar da suka halarci zaman a wannan mako sun hadar da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da Mai ba da Shawara kan Harkokin tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno.
Ministoci 9 ne suka albarkaci zaman da suka hada da; Ministan Kudi, Kasafi da Tsare-Tsaren – Zainab Ahmed; Ministan Ruwa – Suleiman Adamu; Ministan Labarai da Al’adu – Alhaji Lai Mohammed.
Sauran sun hadar da; Ministan Ayyuka da Gidaje – Babatunde Fashola; Ministan Matasa da Wasanni – Sunday Dare; Ministan Harkokin Cikin Gida – Ogbeni Rauf Aregbesola.
Sai kuma Ministan Lantarki – Sale Mamman; Ministan Harkokin Waje – Geoffery Onyeama da kuma Ministan Noma – Sabo Nanono.