Majalisar Wakilai ta zargi Ministar Kudi, Zainab Ahmed da Akanta-Janar na Kasa, Sylva Okolieaboh da Kuma Darakta-Janar na Ofishin Kasafin kudade, Ben Akabueze da yin kafar ungulu ga yaki da rashawa a Najeriya.
Majalisar ta yi zargin ne tare da sanya kalubalantar dalilin ware wa hukumomi masu ‘dumama kujera’ makuden kudade’ a kasafin 2023, amma suka zaftare fiye da rabin kasafin Ofishin Mai Binciken Kudi na Kasa.
- NAJERIYA A YAU: Anya APC ta Shirya Cin Kano A Zaben 2023?
- An cimma yarjejeniyar kawo karshen rikicin Tigray
Hakan ta taso ne bayan mukaddashin Mai Binciken Kudi na Kasa, Andrew Okwudili, ya yi mata korafi cewa Ofishin Darakta-Janar kan Kasafi ya yi wa Ofishinsa kwauron kudi, duk kuwa da “matsayinsa na babbar hukumar bibiyar hukumomin tara kudaden shigar Gwamnatin Tarayya.
“Babbar Hukuma irin wannan tana bukatar isassun kudaden da kayan aiki da duk abubuwan da suka dace domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata,” in ji shi.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake kare kasafin kudin ofishin na 2023 a gaban Kwamitin Kudade na Majalisar Wakilai a ranar Laraba.
An soke rabin kasafin Ofishin Binciken Kudi
Shugaban Kwamitin, Oluwole Oke, da mambobin kwamintin, ya caccaki Ministar Kudi, Zainab Ahmed da Darakta-Janar-janar din, da cewa rage ofishin Daraktan Kasafi da suka yi, wata makarkashiya ce ga yaki da rashawa.
Don haka ya Ministar da Darka-Janar-janar din su bayyana a gaban kwamitin, domin amsa tambayoyi kan dalilin rage kafasin Ofishin.
Okwudili, wanda ya bayyana wa kwamitin cewa kwauron da aka yi wa Ofishin zai hana gudanar da ayyukansa yadda ya kamata ya ce.
Ya ce an zaftare kudaden ma’aikata da ofishin ya gabatar daga biliyan 3.041 zuwa N2.349bn; N5.59bn na ayyukan yau da kullum kuma an rage zuwa N2.113bn sannan an zaftare manyan ayyukan N2.52bn zuwa N62.70m.
Zargin makarkashiya
A martaninsa, Oluwole Oke, ya ce: “Mun lura da mukarraban Shugaban Kasa, Musamman Ministar Kudi da Darakta-Janar na Ofishin Kasafi na yin makarkashiya ga yaki da rashawa a kasar nan.
“Yaya za su ware wa ware wa kananan ciyoyin gwamnati biliyoyin Naira amma ku bai wa Ofishin Mai Binciken Kudi na Kasa miliyan N62 domin gudanar da manyan ayyuka?
“Ofishin ya tantance bukatunsa na ma’aikata da kayan aiki a ofisoshinsa da ke fadin kasar nan sannan ya gabatar da kasafinsa ga Ofishin Kasafi na Kasa;
“Amma Ofishin Kasafi ya yi gaban kansa, ya saba ka’ida, ya rage kudaden manyan ayyuka zuwa N62m, ya zaftare N3bn daga kudaden ayyukan yau da kullum; amma kuma ya bai wa hukumomin da kusan babu abin da suke yi biliyoyin Naira.
“A haka babu abin da zai haka a ce mutanen da shugaban kasa ya nada suna yakar sa; Don haka ba mu amince da kasafin nan ba, domin ba mai yiwuwa ba ne.”
Ya ci gaba da cewa, “Dole Ministar Kudi da Darakta-Janar na Ofishin Kasafi da Akanta-Janar na Tarayya su gurfana domin amsa tambayoyi kan abin da ya sa su yin makarkashiya ga Ofishin Binciken Kudi na Kasa.
“Me ya sa za su ware wa EFCC da ICPC kudade fiye da ofishin? Ba za mu yarda ba.”