✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministar Buhari ta sami mukami a Majalisar Dinkin Duniya

Za ta dai Shugabanci kwamitin bangaren mata

Ofishin Hana Kisan Kiyashi na Majalisar Dinkin Duniya ya nada Ministar Mata ta Najeriya, Pauline Tallen, a matsayin Shugabar kwamitin kiyaye kisan kiyashi ta bangaren mata ta duniya.

Mai taimaka wa Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, a ofishin kiyaye kisan kiyashin, Alice Nderitu, ce ta bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja lokacin da ta ziyarci Ministar.

Alice ta ce a ana sa ran kwamitin zai tsara manufofin yaki da kisan kiyashi a yankunan da ake fama da matsalar, musamman ta bangaren mata.

Ta ce, “Akwai yanayin da ake samu wasu na yunkurin shafe wata kabila, launin fata ko mabiya wani addini daga doron kasa.

“Tambayar a nan ita ce me ya kamata a yi wajen magance wannan matsalar?

“Dalilin ke nan da ya sa na zo wajenki saboda a watan Yuli mai zuwa, za mu gudanar da wani gagarumin taro na mata daga sassa daban-daban na duniya, wadanda za su yi aiki samar da zaman lafiya su kuma rattaba hannu a kan yarjeniyoyin da za a rika amfani da su a matsayin dokokin kasa da kasa da kuma kawo karshen yake-yake,” injin ta.

Ta kara da cewa ana sa ran kwamitin zai kuma gabatar da rahotonsa gaban Babban Zauren majalisar.

Da take mayar da jawabi, Minista Pauline ta gode wa majalisar kan damar da aka ba ta, inda ta ce za ta yi aiki tukuru wajen ganin ta ba mara da kunya.

“Na saurari duk jawabanki, kuma ina godiya. A madadin ni kaina da sauran matan Najeriya, muna nuna godiyarmu da irin wannan karramawar,” inji Minista Pauline Tallen. (NAN)