Ministsan Tsaro, Bashir Magashi, ya jagoranci manyan hafsoshin tsaro zuwa Jihar Borno domin gane wa idanunsu nasarar da ake samu a yakin da ake yi da ta ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
Magashi da tawagar tasa sun sauka a Maiduguri ne ranar Juma’a, inda za su yi ganawar sirri da Babban Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai, Manjo-Jaaar CG Musa da sauran kwamandojinsa.
- ISWAP ta kai hari a sansanin ’yan sanda a Damboa
- An samu ci gaba sosai a harkar tsaro —Shugaban ‘Yan Sanda
Sun kai ziyarar ce washegarin wani hari da mayakan kungiyar ISWAP suka kai garin Damboa a Jihar Borno, suka kashe mutum hudu, cikin har da ’yan sanda uku.
Abokan tafiyar ministan tsaron su ne Babban Hafsan Tsaro, Janar Leo Irabor da kuma Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Faruk Yahya.
Sauran su ne Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Isiaka Amao da kuma Babban Hafsan Sojin Ruwa, Riya Admiral Awwal Gambo.