Ministan Harkokin Cikin Gida na Kasar Estonia, Mart Helme, ya ce zai yi murabus daga mukaminsa biyo baya sukar zababben Shugaban Amurka, Joe Biden.
Mart Helme ya bayyana hukuncin hakan ne yayin tattauna wa da manema labarai a ranar Litinin.
Wannan mataki ya biyo bayan furucin da Mista Helme tare da dansa wanda ya kasance Ministan Kudin kasar, Martin Helme suka yi game da zababben Shugaban Kasar Amurka da aka yi kwanan nan wanda suka alkakanta shi da mai cike da magudi.
Ministan yayin tattaunawa a gidan rediyo a ranar Lahadi ya bayyana zababben shugaban Amurka, Joe Biden da kuma dansa Hunter Biden a matsayin masu cin hanci da rashawa.
Mart Helme ya riki cewa har yanzu Joe Biden bai zama Shugaban kasar Amurka ba, don har yanzu ba a sanar da sakamakon zaben ba a hukumance.
Ya kuma ce a yayin da Joe Biden zai kasance a matsayin Shugaban Amurka, za a samu koma baya ta fuskar ci gaban kasar a karkashin jagorancinsa.
Mista Helme da dansa wanda suka kasance ’yan jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta Consevative People’s Party a Estonia, sun ce sun yarda cewa an yi magudi a zaben Amurka da aka gudanar a ranar 2 ga watan Nuwamba.
Firaiminista Juri Ratas da Shugabar Kasar Estonia, Kersti Kaljulaid sun yi Allah wadai da kalaman ministocin biyu inda Kersti ta ce sun ba ta kunya.