Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan Maryam Shetty da na Mariya Mahmoud a matsayin minista daga Kano.
Da safiyar Juma’a ne shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio ya sanar da wannan sauyin a zauren Majalisar.
A ranar Laraba ne dai shugaba Tinubu ya bai aike wa Majalisar sunan Maryam Shetty a matsayin ɗaya daga cikin ministocin da zai naɗa daga Kano.
Sai dai naɗinta ya jawo cece-kuce musamman a soshiyal midiya kasancewar abin ya zamo ba-zata.
Wacece Mariya Mahmoud?
Dr Mariya Mahmoud ita ce kwamishinar ilimi mai zurfi a zamanin gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Kafin zama kwamishina kuma likita ce a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.