Ministar Kwadago da Jinkai ta kasar Cuba, Marta Feito Cabrera, ta sauka daga mukaminta bayan ta ce babu mabarata a kasar, sai dai masu karyar kasancewa mabarata.
Fadar Shugaban Kasar a ranar Laraba ta sanar da cewa Ministar ta amsa kuskurenta sannan ta mika takardar ajiye aiki kan abin da ta kira “nuna rashin rashin tausayi da rashin kwarewa a kan batun da yake da tasiri a siyasance a kasar.
- DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari
- Dangote zai gina tashar jiragen ruwa mafi girma a Najeriya a jihar Ogun
Labarin dai na zuwa ne kwana daya bayan Ministar ta yi kalaman a gaban ’yan kwamitin majalisar kasar a kan talauci a kasar wacce tsibiri ce.
Marta dai ta ce, “Mun ga mutane, wadanda a Zahiri mabarata ne, amma idan ka kalli hannunsu, ka duba tufar da ke jikinsu, za ka ga sun yi bad-da-bami a matsayin mabarata, amma ba mabarata ba ne.
“A Cuba, babu mabarata,” in ji ta.
Ta kuma ce mutanen da ke wanke wa masu motoci gilashin motocinsu a kan titi suna rayuwa mai sauki, kuma sukan yi amfani da abin da suka samu wajen sayen barasa.
Nan take kalaman nata dai suka karade gari, musamman a shafukan sada zumunta, inda aka rika kiraye-kirayen ta ajiye mukaminta.
Kasar Cuba dai na cikin mawuyacin halin matsin tattalin arziki a ’yan shekarun nan.
Hatta Shugaban Kasar, Miguel Diaz-Canel sai da ya soki lamirinta.
Kasar dai ta shiga kangi ne tun bayan wani takunkumin tattalin arziki da Amurka ta kakaba mata a shekarar 1960, lokacin da Fidel Castro ya jagoranci juyin juya hali a kasar.