Tsohon Sanata Elisha Abbo, wanda ya wakilci Adamawa ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya ce Naira miliyan 29 da Sanatoci ke karɓa duk wata, ba kuɗi ne da suka taka kara suka karya ba.
Ya bayyana cewa lokacin da yake sanata, yana samun Naira miliyan 14.4 a wata, amma yanzu ‘yan majalisar dattawa suna karɓar Naira miliyan 29.
- An tsinci gawar ɗan sandan da aka sace a Filato
- Tinubu ya bayar da umarnin biyan tallafin man fetur – Rahoto
Abbo, ya bayyana cewa kuɗaɗen ba za iya biyan buƙatun sanata ba.
Ya ce ya bar kasuwancinsa don ya zama sanata, amma hakan ya sa ya zama talaka saboda ya kan yi amfani da kuɗinsa don taimaka wa al’ummar mazaɓarsa.
Ya bayar da misali, inda ya kashe Naira miliyan 14 don taimaka wa wani mutum wajen magani, kuma sau da yawa yana neman taimako daga gwamnoni domin biyan buƙatun mutanen yankinsa.
A baya-bayan nan, tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya soki ‘yan majalisar kan yanke wa kansu albashi da alawus mai gwaɓi.
Sai dai Majalisar Dattawa ta musanta waɗannan zarge-zargen, kuma Hukumar Rarraba Kuɗaɗen Shiga da Kula da Kasafin Kuɗi (RMAFC), ta fayyace cewa kowane sanata na karɓar Naira miliyan 1.6 a wata a matsayin albashi da alawus.