A watan jiya ne Kwamandan Yaki da Boko Haram da aka fi sani da Joint Task Force Operation Hadin Kai ya sanar da cewa akalla mayakan Boko Haram da ISWAP da iyalansu 70,593 ne suka mika wuya bayan sun ji wuta daga jami’an tsaro.
An fara yakin Boko Haram ne a watan Yulin shekarar 2009 bayan kashe Shugaban Boko Haram na wancan lokacin, Muhammad Yusuf.
- Gwamnati ta ba dan kwangila wata 4 ya kammala aikin titi a Kano
- FBI ta bankado bayanan sirri 11 a gidan Trump
Daga lokacin zuwa yanzu shekara 13 ke nan ana fafata yakin, inda ake samun kwan-gaba-kwan-baya wajen murkushe ’yan ta’addar.
Rikicin Boko Haram ya mamaye jihohin Arewa maso Gabas da wasu jihohin Arewa, sai dai za a iya cewa yanzu an samu sanarar dakile su a yankin dajin Sambisa.
Rikicin ya ci dubban mutane, inda a wani rahoto da Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa rikicin ya ci kananan yara akalla 300,000.
A bayanin na Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, daga cikin mutum 70,593 da suka mika wuya, mutum 14,609 mayaka ne na kungiyoyin ta’addancin guda biyu, sai mata 20,955 da yara 35,029.
‘Dole ta sa suke mika wuya’
Tun a farkon bana wata majiyar tsaro ta bayyana wa Aminiya cewa dole ta sa ’yan ta’addar suke mika, sannan ta ce da yawansu ma za su ci gaba da mika wuya domin babu yadda za su yi.
“Muna ci gaba da yakarsu. Ina tabbatar maka cewa ba kamar yadda aka saba ba ne, domin abubuwa da dama da suke kawo mana cikas a wannan yakin an magance su,” inji majiyar a wancan lokaci.
A cewarta daga cikin abubuwan da suka suke samun nasara akwai amfani da jiragen yakin Super Tucano da sauransu.
Sai dai ta ce ana samun jinkiri ne saboda a tare da mayakan, akwai mata da kananan yara da babu ruwansu da bai kamata a kashe su ba, wanda hakan ya sa ba su cika son jefa bama-bamai a kansu ba.
Tubabbun ’yan ta’addar sukan yaudari mutane – Hakimin Chibok
Sai dai tun a bara da aka fara murnar mika wuya da ’yan ta’addar suke yi, Hakimin Chibok, Injiniya Zanna Modu ya ce ya kamata a lura sosai ko akwai lauje cikin nadi a lamarin tubar.
Ya ce, “Duk da cewa abu ne mai kyau, su mika wuyan, amma ya kamata a bi lamarin da tsanaki domin an sha samun hakan.
“Mukan samu inda mutum zai je ya tuba, amma daga baya ya koma daji ya ci gaba da ta’addancinsa. A ce mutum ya tuba ya mika wuya ba tare da ya kawo bindigarsa ba, akwai alamar tambaya.
“Ni a tunanina, duk dan Boko Haram da ya kashe mutane, to kawai a kai shi kotu ya fuskanci shari’a.
“Na san dukkan addinai suna koyar da yafiya, amma yafiya irin wannan aba ce mai wahala domin dasun samu dama, da sun karar da mu duka yanzu.
“Ina ba gwamnati shawara ta san yadda za ta dauke su na tsawon lokaci ba tare da wadanda abin ya shafa suna ganinsu ba,” inji Hakimin.
Lokutan da suka fi mika wuya
Binciken Aminiya ya gano cewa da yawa daga cikin mayakan da suka mika wuya sun gudo ne sanadiyar hareharen da jami’an tsaro suke kai musu a sansanoninsu, wadanda suke sa su gudowa cikin gari su mika wuya.
A tsakanin 1 zuwa 14 ga Mayun bana, ’yan Boko Haram 1,627 ne suka mika wuya ga jami’an tsaron Najeriya. Daga cikinsu akwai mayaka 331 da mata 441 da yara 855.
A ranar 13 ga Yulin bana, manyan kwamandojin ’yan ta’addar shida suka ajiye makamai suka mika wuya.
Kwamandojin wadanda suka dade suna addabar yankin su ne: Mala Hassan wanda Gwamna a tsarin kungiyar ta’addancin, sai Babban Kwamanda Jafar Hamma da Musa Bashir da Ali Madagali da Buba Dahiru da Munzur, sai Abbali Nakib Polisawa.
Haka a tsakanin 1 zuwa 14 ga Yulin bana kawai, mayakan Boko Haram da iyalansu 3,858 da suka mika wuya a Jihar Borno.
Su ma a kashe su kawai – ’Yan gudun hijira
Aminiya ta ziyarci sansanonin ’yan gudun hijira da dama domin jin ta bakin mazaunansukan yadda suke ji game da mika wuyan da ’yan ta’addar suke yi.
A sansanin ’yan gudun hijira na Elbadawy, wanda yawanci mutane ne da Boko Haram suka tarwatsa daga kauyen Mijigini, wani mai suna Bakura Mustapha, ya ce ’yan ta’addar sun kashe masa mahaifi da ’yan uwa uku, sannan suka raba shi dasauran ’yan uwansa da har yanzu bai san inda suke ba.
A cewarsa, “Me ya sa za ka fuskance ni da maganar a yafe wa wadannan ’yan ta’adda da suke fake da addini suka cutar da mu. Kana nufin duk barnar da suka yi ta tafi a banza?
“Maganar yafe wa ’yan ta’adda siyasa ce kawai, kuma ba za ta haifar da da mai ido ba, domin nan gaba kadan duk wanda ya ga dama zai dauki makami ya kashe mutane.
“Don haka dole duk wani dan ta’adda da ya kashe mutane ya fuskanci doka domin ya zama izina,” inji shi.
Mutapha ya kushe Gwamnatin Jihar Borno kan daukar wannan mataki, “Ban san me ya sa gwamnati ta dauki wannan mataki ba domin akwai rudani.
“Akwai bambanci tsakanin mika wuya da tuba. Wa ya fada musu cewa ’yan ta’addar nan suna tuba kuma sun sauyawa daga mugun tunanin da Boko Haram suka sa musu?
“Su kansu jami’an tsaron suna cewa yawancinsu suna mika wuya saboda sun ji wuta da yunwa da wahala,” inji shi.
Shi ma wani mazaunin sansanin gudun hijira, Aliyu Modu ya ce, “Me ya sa gwamnati take batun yafiya da karbar wadanda suka tuba? Sun manta da ta’addancin da suka yi ne?
“Ban yarda da wannan lamari ba, musamman ganin yadda lamarin ke daukar hankalin ’yan jarida. Maganar gaskiya ya kamata su fuskanci hukunci ne kamar yadda suka kashe mutane.
“Ba za mu yafe musu ba. Ba a maganar halin da muke ciki, sai dai maganar su wadanda suka jefa mu a cikin bala’in. Dole su fuskanci hukunci daidai da laifinsu,” inji shi.
Shi ma Babagana Goni wanda ya gudo daga Karamar Hukumar Mafa, zuwa Maiduguri ya ce, “Akwai asalin ’yan Boko Haram da suka hakikance, akwai kuma wadanda suka shiga domin tsoro.
“Allah da Ya halicci duniya, Ya sa dokoki. Duk wanda ya aikata laifi, akwai hukunci daidai da laifinsa. Amma Allah Ya bayar da damar yafiya da tuba.
“Don haka ina da tunanin a ba da dama ga wadanda da kansu suka mika wuya suka ce sun tuba. Hakan zai taimaka wajen rage karfin ’yan ta’addar.”
Wata mai suna Bintu Mala ta ce, “Wasu daga cikinsu ba da gaske suke tuba ba. Suna mika wuya ne saboda an kashe musu kwamandojinsu, sannan sojoji sun tarwatsa su.
“Idan aka bar su za su iya komawa cikin daji ko su zama masu kai bayanai ga ’yan ta’addar kan harkokin mutane.”
Wannan dama ce ga gwamnati – Masani
Wani mai sharhi kan harkokin yau da kullum, Mohammed Kareto ya ce ganin an dade ana fafata rikicin Boko Haram, wannan tuba wata dama ce ga gwamnati da za ta iya kawo karshen lamarin baki daya.
Koreto ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Aminiya a kwanakin baya lokacin da wasu ’yan Boko Haram suka mika wuya ga jami’an tsaro.
Ya ce ’yan ta’addar suna mika wuya ne saboda sun fara gajiya kuma an fara fatattakar su da kuma rarrabuwar kai da suke ciki tun bayan kashe Shekau.
“A fili yake dakarun Najeriya suna samun nasara a kan ’yan ta’addar. Sai dai ina ba da shawarar kada a yi gaggawar dawo da tubabbun ’yan ta’addar nan cikin mutane domin zai yi wahala mutane su karbe su cikin sauki.
“Ana samun haka dama, wani bangare ya gaji da yaki ya ajiye makami, amma maganar gaskiya amincewa da tubabbtun ’yan ta’adda sai an bi a hankali.
“Ya kamata a bi diddigi a gano wadanda da karfi da yaji aka tursasa su suka shiga ta’addancin kamar ’yan matan Chibok da kuma wadanda su asalin ’yan kungiyar ce da suka yi imani da tafiyarta sannan a tantace su a raba su sannan a rika bibiyansu,” inji shi.
Akwai kuskure a tsarin dawo da su gari – Zagazola
Zagazola Makama fitaccen mai sharhi ne a kan harkokin Boko Haram, ya ce Gwamnatin Tarayya da ta Borno sun shiga kauce hanyar da ya kamata su bi wajen sake dawowa da tubabbun ’yan Boko Haram din cikin mutane.
“Akalla tubabbtun ’yan Boko Haram ne aka zaunar a Karamar Hukumar Bama, inda aka ba wasu dan abin dogaro da kai, wasu ma ba a ba su komai ba.
“Mutanen nan don dole yanzu sun fara bi ta bayan fage suna alaka da tsofaffin abokan ta’asarsu a Sambisa.
“A watan jiya ma wasu mutum takwas sun mutu bayan bam ya tashi wajen sayar da karafa a tsakanin tubabbun da ’yan Boko Haram din. Kuma harkokin bata-gari sun karu a yankin Bama.
“Haka sojoji sun sake kama wasu tubabbun suna taimakon ’yan Boko Haram ta hanyar kai musu bayanai ko abinci da sauran abubuwan bukata.
“A ganina hanyar da aka bi ne aka yi kuskure. Ya kamata a ce an dauki akalla shekara biyu ne suna killace kafin su fara dawowa cikin mutane, ba wata bakwai ba, kamar muka gani.
“Kuma gwamnati ta sa kowane bangare a cikin lamarin, sannan a kafa kwamitoci a kowane yanki don duba manyan ta’adin da aka yi da mutane ba za su yafe ba domin abin da ke faruwa shi ne mutane da dama da abin ya shafa ba a sa su a cikin matakan da ake dauka,” inji shi.