✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mijina bai saci kuɗin Nijeriya ba — Maryam Abacha

Marigayi Janar Sani Abacha ya jagoraci Nijeriya ne ƙarƙashin mulkin soji tsakanin 1993 zuwa 1998.

Uwargidan tsohon shugaban Nijeriya, Maryam Abacha ta musanta zarge-zargen da ake yi wa mijinta na wawure maƙudan kuɗaɗen ƙasar a lokacin da yake kan karagar mulki.

A wata hira da aka yi da ita a kafar talabijin ta TVC a yayin cika shekara 27 da rasuwar Abacha, Maryam ta nanata cewa bai sace kuɗaɗen Nijeriya, tana mai cewa, da gangan aka sauya manufarsa ta adana dukiyar ƙasar a ƙetare.

 Maryam Abacha ta ƙalubalanci waɗanda ke zargin mijinta da wawure dukiyar talakawa da su gabatar da gamsasshiyar hujja kan zarge-zargensu, tana mai ɗiga ayar tambaya kan wane ne shaida kan kuɗaɗen da aka adana su?

“Shin ka ga sanya hannu ko wata hujja kan dukiyar da aka adana? Kuɗin da mijina ya ɓoye saboda amfanin ’yan Najeriya, sun yi batar-dabo cikin ’yan watanni. Mutane ba sa magana a kan wannan.”

Kazalika Maryam Abacha ta ce, “me ya sa ake caccakar mutum? Shin ana yin haka ne saboda ƙabilanci ko banbancin addini? Mece ce matsalar ’yan Najeriya?”

Maryam ta kuma caccaki ’yan Nijeriya kan yadda suka yi amanna da abubuwan da gwamnatocin bayan suka faɗa musu na cewa, sun karɓo kuɗaɗen da Abacha ya zuba su a asusun ƙasashen ƙetare.

Gwamnatocin Nijeriya daban-daban da aka yi, sun yi nasarar karɓo ɗaruruwan miliyoyin dala da aka adana su a asusun ƙasashen ƙetare bayan an ce Abacha ne ya sace su tare da ajiye a waje.

Ƙasashen da aka karɓo kuɗaɗen sun haɗa da Switzerland da Amurka da Birtaniya, inda aka yi amfani da su a wasu shirye-shiryen raya al’umma.

Marigayi Janar Sani Abacha ya jagoraci Nijeriya ne ƙarƙashin mulkin soji tsakanin 1993 zuwa 1998.