Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce ta kashe ’yan ta’adda da dama a cikin wasu jerin hare-hare na sama da na ƙasa da suka kai sansanonin ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP da ke Nzalgana, a ƙaramar hukumar Gujba ta Jihar Yobe a Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce hare-haren da sojojin suka ƙaddamar da sanyin safiyar Litinin 9 ga watan Yuni sun yi sanadin mutuwar wani babban kwamandan Boko Haram a ƙauyukan Ngorgore da Malumti, Ameer Malam Jidda.
- Zai fi kyau Tinubu ya mayar da hankali kan ’yan Nijeriya ba Zaɓen 2027 ba — ACF
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba
Duk da cewa sanarwar ba ta yi ƙarin bayani game da jerin hare-haren ba, sai dai Zagazaola Makama, wani kwararren kan lamuran tsaron a yankin, ya ruwaito cewa sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK47 da harsasai da kuma babur daga hannun kwamandan da aka kashe.
Sai dai kuma sanarwar ta sojojin ta bayyana cewa sojojin sun sake samun ƙarin makamai da gawarwakin ‘yan ta’adda a Abadam bayan arangamar da suka yi da ‘yan ta’addan kwanan nan a Mallam Fatori.
Cikin ‘yan makonnin nan dai an yi ta samun rahotannin hare-haren da ‘yan ta’adda ke kai wa sansanonin sojoji a yankin.
Kazalika sojojin ƙasar su ma suna kai hare-hare ta sama kan sansanonin ‘yan ta’addan a yankin domin su hana su iya kai irin hare-haren da suke kai wa kan sojoji.