Yarima Philip, mijin Sarauniyar Elizabeth II ta Ingila ya rasu a Fadar Buckingham bayan shekara 99 a duniya.
Fadar Buckingham ta tabbara da rasuwar Yarima Philip, wanda shi ne Magajin Garin Edinburgh a ranar Juma’a 9 ga Afrilu, 2021.
- Sojoji sun kashe mutum 70 a wani samame a Binuwai
- Matar aure mai sana’ar tuka keken ’A Daidaita Sahu’ a Kano
- Dalibi ya yi doguwar suma bayan yi masa bulala 6,000
- An gano bom a makarantar firamare a Abiya
“Cikin alhini da kaduwa, Mai Alhfarma Sarauniya na sanar da rasuwar mijinta, Mai Martaba Yarima Philip, Duke na Edinburgh lami lafiya…” inji sanarwar da ta ce nan gaba za a bayyana tsare-tsaren jana’iza da zaman makokin mamacin.
A watan Fabrairu aka fara kwantar da Yarima Philip a asibiti a birnin London sakamakon ciwon zuciya, kafin daga bisani a sallame shi a sakiyar watan Maris, bayan an yi masa tiyata.
A ranar 10 ga watan Yuni, 1921 ne aka haifi Yarima Philip a Tsibirin Corfu na kasar Girka.
Iyayensa su ne Yarima Andrew na Girka da Denmark —dan Sarki George I— da kuma Gimbiya Alice, ’yar Lord Louis Mountbatten.
A shekarar 1947 Yarima Phikip ya auri Gimbiya Izabel, shekara biyar kafin ta zama Sarauniyar Ingila.
Ma’auratan, su ne suka fi dadewa a kan karagar mulki a tarihin Masarautar. Allah Ya azurta su da ’ya’ya hudu da jikoki takwas da tattaba kunne 10.