Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari kan zargin barazana ga rayuwar matarsa da yake zargin ta da maita.
Babbar Kotun Musulunci da ke Gazawa a Jihar Kano ta tsare mutumin ne bayan ya yi barazana tare da yunƙurin kai wa matar tasa farmaki da adda.
Mai gabatar da ƙara, Sadiq Yusuf ya shaida wa kotun cewa mutumin ya yi yunƙurin aika-aikan ne bisa zargin matarsa da kama kuruwar ɗansu da ya jima yana fama da rashin lafiya.
Magidancin da ke zaune a ƙauyen Gawo da iyalin nasa ya musanta tuhumar da ake masa, don haka, Alƙali Nura Ahmad ya ba da umarnin tsare shi a gidan yari.
- Bidiyon batsa: Kotu ta ɗaure ’yan Tiktok a gidan yari a Kano
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba
Ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan nan na Maris domin masu ƙara su gabatar da shaidu.
Ɓari: Matan aure sun yi wa wata barazana
A wata sabuwa kuma, an gurfanar da wasu matan aure biyu kan zargin yin barazana ga wata da suke zargi da haddasa zubewar juna biyun dayarsu.
Kotun da ke zamanta a unguwar Danbare, Ƙaramar Hukumar Kumbotso, na zargin matan auren da haɗa baki da yunƙurin aikata laifi.
Ana zargin matan waɗanda mazauna unguwar Rimin Auzinawa da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo da barazanar ga matar tare da zargin ta da haddasa zubewar juna biyun dayarsu.
Sai dai sun musanta zargin, inda daga baya alƙalin, Khadi Munzali Idris Gwadabe, ya ba da belinsu, bayan lura da yanayin lafiyar wadda ta yi ɓarin, da ke murmurewa.
Ya kuma daga sauraron shari’ar zuwa ranar 16 watan Afrilu.