Wani matashi mai suna Abdulkadir Abubakar Iya da ke garin Zangon Kataf a Jihar Kaduna ya kada wani likita har kasa bayan ya shaida masa cewa matarsa ta cika bayan yi mata aiki a Babban Asibitin Kafanchan, saboda zargin likitan da yi mata fida ba tare da sa hannunsa ko wani madadinsa ba kamar yadda doka ta tanada.
Mijin marigayiyar ya shaida wa Aminiya cewa bayan awa guda da fara nakudar matarsa Hajara Isa, sai ya garzaya da ita Babban Asibitin Zangon Kataf, amma bayan duba ta da wasu nas-nas suka yi sai suka shaida masa cewa aikin ya fi karfinsu sai dai likita. “Mun je mun yi ta buga masa kofa yana barci. Da muka ga lokaci zai kure mana ga shi bai tashi ba sai sauran nas din suka ba mu shawarar mu kai ta asibitin Kafanchan don shi ne mafi girma a Kudancin Kaduna. Abin ya faru ranar Asabar ce, bayan mun kawo ta har zuwa Litinin ba ta ci komai ba sai na tambaye su ko za mu iya ba ta shayi ganin cewa ba ta sa komai a bakinta ba kwana biyu kuma ba mu san ko za su bukaci yi mata aiki ba. Bayan mun ba ta ta sha da saninsu zuwa can sai suka bukaci karin jini. Ni da dan uwana mun je inda za a gwada jininmu a diba, to muna dawowa sai kawai ba mu gan ta a dakin da take kwance ba. A tsorace na tambayi ko ina take sai aka ce an shigar da ita dakin tiyata. Na tambaya ko wa ya sa hannu a madadina kafin a shigar da ita, duka ’yan uwana babu wanda ya sa hannu. Muna tsaye zuwa can sai na ga an fito ana tambaya su wane ne ’yan uwanta? Sai na ce gani, kawai sai na ji an ce wai mu yi hakuri wance ta rasu sakamakon shayin da muka ba ta kafin a yi mata aiki,” inji shi.
Ya kara da cewa “A lokacin ban san lokacin da na rarumi likitan na buga shi da kasa ba saboda gaskiya ba a yi min adalci ba. Ta yaya zan tambaye su in ba ta shayi bayan sun amince kafin in ba ta sannan su shigar da ita aikin fida ba tare da sa hannuna ba, kuma a karshe su ce mini wai shayin da na ba ta ne ya yi ajalinta?”
Bayan tashin hayaniyar ne nan da nan malamai da ’yan sanda a karkashin DPO Baba Ali suka kawo dauki kafin lamarin ya zama wani abu daban.
Marigayiya Hajara Isa ba su dade da yin aure ba kuma wannan ita ce haihuwarta ta farko.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi Shugaba kuma Babban Likitan Asibitin, Dokta Jonathan Gajere ta waya kan lamarin bai amsa wayar ba.
A karshe Abdulkadir Iya, mijin marigayiyar ya ce duk da an zalunce shi amma ya bar wa Allah komai.