Babbar Kotun Jihar Kano ta 6 da ke Titin Miller ta yanke wa Aminu Inuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun shi da laifin kashe matarsa a kan dumame.
Aminu, wanda mazaunin Unguwar Gwazaye ne da ke Dorayi Babba a Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, sun samu sabani da matarsa Safara’u Mamman ne a kan dumamen tuwo wanda hakan ya sa ya dauko wuka mai kaifi ya yanka makwogoronta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta.
- Na sa an sace babana an kashe shi, aka ba ni N2,000 —Danbindiga
- Miji ya kashe matarsa saboda koko a Neja
Aminu Inuwa, wanda kotun ba ta bayyana shekarunsa ba an yanke mishi hukuncin ne bisa samun shi da aikata laifin kisa wanda ya saba da Sashe na 221 na Kundin Final Kod.
Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai shari’a Usman Na’abba, ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun gamsar da kotu da hujjojinsu, don haka kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Tun farko, lauyan gwamnati mai gabatar kara, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya shaida wa kotun cewa a ranar 2 ga Afrilun 2019, Aminu Inuwa ya kashe matarsa a Unguwar Gwazaye.
“A wannan rana da misalin karfe 10:00 na rana, Aminu Inuwa ya samu rashin fahimta da matarsa Safara’u.
“A daidai wannan lokaci ne sai ya yi amfani da wuka mai kaifi ta kicin inda ya yanka wa matar tasa makwogoro, lamarin da ya yi sanadiyyar muturwarta.
“Bayan ya kashe ta kuma sai ya binne gawarta a cikin wani daki da ba a kammala gininsa ba a cikin gidan,” inji lauyan.
A lokacin gudanar da shari’ar, masu gabatar da kara sun gabatar wa kotun shaidu uku tare da hujjoji shida don tabbatar da laifin kisan a kan wanda ake zargi.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake zargin shi da shi, amma ya gaza gabatar wa kotu kwakkwarar shaida a kan haka.