✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Microsoft ya sa kafar wando daya da Amurka

A shekaranjiya Laraba ne kamfanin Miscrosoft ya koma kotu domin ci gaba da rikicin da yake game da bukatar gwamnatin kasar Amurka na cewa ya…

A shekaranjiya Laraba ne kamfanin Miscrosoft ya koma kotu domin ci gaba da rikicin da yake game da bukatar gwamnatin kasar Amurka na cewa ya mika wasu sakonnin e-mail da yake ajiye da su a wata cibiyar tattara bayanai da ke kasar Ireland, kamar yadda gidan rediyon  BBC ya bayyana.
A bara ne wata kotu ta yanke hukuncin da ya goyi bayan ikirarin da gwamnatin Amurka ta yi na cewa saboda tana da hurumi a kan kamfanin da ke da ofis a Amurka, za ta iya tilasta masa mika mata bayanan da yake da iko da su ko da ace a wata kasar ake ajiye da su.
Amma kamfanin Microsoft ya ba da shawarar cewa hakan ya saba wa dokokin sirri.
A madadin haka kamfanin ya ce dole ne kasar ta mutunta ‘yancin wasu kasashe sannan ya nuna alamun cewa Washington ta yi amfani da yarjejeniyar taimakon alkalai idan har tana son samun sukunin wadannan bayanai daga kasar Ireland da kuma wasu cibiyoyin tattara bayanai da ke wajen Amurka.
Tuni kasar Ireland ta ce tana duba wannan bukata cikin gaggawa.
Wannan sa-in-sa na nuna karfin da Amurka ke da shi a kan kamfanonin da ke kasarta.