Kamfanin Meta ya ɗage takunkumin da ya sanya wa shafukan tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump na Facebook da Instagram, gabanin shiga babban zaɓen ƙasar a watan Nuwamba.
An dakatar da shafukan nasa ne a 2021 bayan ya yaba wa magoya bayansa da suka kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin ƙasar a ranar 6 ga watan Janairu.
- An cinna wa fadar Sarki Sanusi II wuta a Kano
- Shekara 100 a duniya: Sheikh Dahiru Bauchi ya sake kafa tarihi
An sake dawo da su a bara amma bisa tsattsauran sanya ido, tare da barazanar sake dakatar da su idan Trump ya keta ƙa’idojin da aka sanya.
Yanzu dai an cire waɗannan sharuɗan.
Meta, ya ce yana da alhakin bayar da damar bayyana ra’ayoyin siyasa kuma ya kamata Amurkawa su ji ta bakin waɗanda ke son zama shugabanninsu.
Trump, wanda aka samu da laifi, a baya an haramta masa amfani da Twitter da kuma YouTube.
A baya Trump ya kan yi amfani da dandalinsa na ‘Truth Social’ wajen aike wa magoya bayansa saƙo.