✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi yana fama da cutar koda

Bayanai sun nuna shahrarren dan kwallon Ajantina da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi yana fama da…

Bayanai sun nuna shahrarren dan kwallon Ajantina da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi yana fama da cutar da ta shafi kodarsa (Kidney).
A wata sanarwa da kulob din Barcelona ya fitar a ranar Lahadin da ta wuce ta nuna sai da Messi ya koma asibiti a ranar Litinin da Talatar da suka wuce inda Likitoci suka sake duba lafiyarsa a kan cutar kodar da yake fama da ita.
Kulob din ya ce dan kwallon ya kamu da cutar ce tun a watan Disambar 2015, al’amarin da ya sa bai buga wadansu daga cikin wasannin da kulob din ya yi a gasar cin kofin Club World Cup da ya gudana a Japan ba.
Sai dai tuni dan kwallon ya murmure  kuma ya ci gaba da yi wa kulob din wasa, hasalima yana daga cikin ’yan kwallon kulob din da za su fafata da kulob din Celta-bigo a gasar La-Liga ta Sifen a jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu.