✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya zargi Manchester United a wasansu da AS Roma

dan kwallon gaba a kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi a shekaranjiya Laraba ya dora alhakin ficewarsu daga gasar zakarun kulob na Turai…

dan kwallon gaba a kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi a shekaranjiya Laraba ya dora alhakin ficewarsu daga gasar zakarun kulob na Turai bayan AS Roma na Italiya ta lallasa su da ci 3-0 a kan kulob din Manchester United na Ingila a game da yadda kulob din yake zawarcin dan kwallon bayansu Samuel Umtiti a wannan lokaci.

Ya ce yadda kulob din yake zawarcin dan kwallon a wannan lokaci, ya taimaka wajen kawar masa da hankali a wasan, da hakan ta sa ’yan kwallon Roma suka yi amfani da damar wajen zura masu kwallaye har uku ba tare da sun mayar da martani ba.

“A gaskiya yadda kocin United Jose Mourinho ya nuna sha’awar dauke Umtiti a karshen kakar wasa ta bana na daga cikin dalilan da ya sa AS Roma ta fitar da mu a gasar.”

Masoya kwallon kafa musamman magoya bayan kulob din FC Barcalona sun kadu game da yadda kulob din AS Roma ya fitar da na FC Barcelona daga gasar duk da Barcelona ce ta samu nasara a wasan farko da ci 4-1.

Haka kuma Messi ya zargi dan kwallon baya Jordi Alba a wasan, inda ya ce dan kwallon bai yi kokari ba.  Ya ce bayan an tafi hutun rabin lokaci, sai da ya janyo hankalin Umtiti da Jordi a kan su mayar da hankali a wasan, amma duk da haka ba su dauki shawararsa ba har  hakan ta faru.

Sai dai magoya bayan Barcelona suna zargin Messi da sauran ’yan kwallon wajen yin sakaci har Roma ta yi kaca-kaca da hakan ta sa aka fitar da su a gasar.

Yanzu dai AS Roma ta haye matakin kusa da na karshe (semi-fainal) inda take jiran kungiyar da za a hada ta da ita a jadawalin da Hukumar UEFA za ta yi a yau Juma’a.