A ranar Litinin da ta gabata ne aka zabi shahararren dan kwallon kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi a matsayin gwarzon dan kwallon gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga na shekarar bara.
An zabi Messi ne a matsayin dan kwallon gaban da ya fi nuna kwazo kuma ya fi zura kwallaye a raga a yayin gasar ta shekarar da ta gabata. Kuma ya doke abokin takararsa Cristiano Ronaldo, dan kwallon Real Madrid ne a fafatawar da suka yi.
Messi wanda yana daga cikin ’yan kwallon uku da za su kara a Gwarzon dan kwallon duniya, ya lashe wannan kyauta sau shida a tsakanin shekara 7 da aka fara yin ta a Sifen.
dan kwallon ya zura kwallaye 43 a raga a yayin gasar a bara, al’amarin da ya sa ya taimaka wa kulob din FC Barcelona lashe kofunan La-Liga da na zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) da kofin Sifen da sauransu.
“Na yi murna da na samu wannan kyauta bayan na sha gaban zaratan ’yan kwallo da yawa a gasar La-Liga”.
“Na sadaukar da wannan kyauta ga dana Thiago (dan shekara 3) duk da bai gama yin wayau ba. A duk lokacin da na shirya zan tafi filin kwallo yakan tambaye ni, Baba za ka tafi filin kwallo don ka zura kwallo a raga ne?, sai na yi murmushi kafin na fita, saboda haka na sadaukar da wannan kyauta a gare shi”, inji shi.
Kyaftin-kyaftin na kungiyoyin da ke fafatawa a gasar La-Liga ne suka kada kuri’unsu a zaben.
Golan Barcelona Claudio Brabo ne aka zaba a matsayin golan da ya fi nuna kwazo yayin da aka zabi Sergio Ramos da James Rodriguez ’yan kwallon Real Madrid a matsayin wadanda suka fi yin kokari a dan kwallon baya da kuma dan kwallon tsakiya bi-da-bi a gasar.
Messi ya zama Gwarzon dan kwallon La-Liga
A ranar Litinin da ta gabata ne aka zabi shahararren dan kwallon kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi a matsayin gwarzon dan kwallon…
