✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya zama Gwarzon dan kwallon Duniya a karo na biyar

A ranar Litinin da ta gabata ne shahararren dan kwallon Ajantina da kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi ya zama Gwarzon dan kwallon…

A ranar Litinin da ta gabata ne shahararren dan kwallon Ajantina da kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi ya zama Gwarzon dan kwallon Duniya a karo na biyar.
Ya doke abokan takararsa Cristiano Ronaldo na Real Madrid da kuma Neymar na FC Barcelona ne a lokacin da suka fafata neman wannan matsayi a hedkwatar Hukumar FIFA da ke Zurich.
Messi, ya samu kashi 41.33 na yawan kuri’un da aka kada ne da hakan ya ba shi damar lashe kyautar yayin da mai biye da shi Cristiano Ronaldo ya samu kashi 27.76 na yawan kuri’un da aka kada.  Sai Neymar wanda ya samu kashi 7.86 a matsayin kuri’un da aka kada masa, kuma shi ne na uku.
Yanzu Messi ya zama dan kwallo daya tilo da ya taba lashe wannan kyauta har sau biyar a tarihinta.
Ronaldo ne ya lashe sau biyu a jere watau a shekarar 2013 da 2014 kuma karo na uku a jimilla.  Lionel Messi kuma ya lashe kyautar ce a shekarun 2009 da 2010 da 2011 da kuma a 2012 sai kuma a wannan karo 2015 da ya lashe na biyar.
A jawabin da ya yi jim kadan bayan ya karbi kyautar Messi ya nuna farin cikinsa a game da sake lashe gasar a karo na biyar.  Sannan ya yabawa takwarorinsa a FC Barcelona wadanda ya ce da taimakon su ne ya samu wannan nasara, inda ya jinjina musu.
Sannan ya gode wa wadanda suka jefa masa kuri’ar da ta sa ya lashe wannan gasa.  Daga nan kuma ya yaba wa harkar kwallo, inda ya ce kwallo ce ta sa ya samu daukaka a duniya.
Kocin kulob din Barcelona Luis Enrikue ne aka zaba a matsayin Gwarzon Kocin 2015.