✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Messi ya kamu da Coronavirus

Messi ba zai buga wasan da PSG za ta yi ba a ranar Litinin.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Paris Saint Germain ta sanar da cewa ’yan wasanta hudu sun kamu da cutar Coronavirus ciki har da tauraronta, Lionel Messi.

Sauran ’yan wasan da PSG ta sanar da cewa sakamakon gwaji ya nuna sun harbu da cutar sun hada da Juan Bernat, Sergio Rico da Nathan Bitumazala.

A bayan nan dai sabon nau’in cutar Coronavirus da ake kira Omicron ya sa manyan’ yan wasa da dama da kuma koca-kocai suna rasa damar halartar wasanni.

A halin yanzu dai PSG za ta halarci wasan da za ta fafata da Vannes a gasar Coupe de France a ranar Litinin ba tare da mai horas da yan wasanta ba, Mauricio Pochettino da kuma jigo cikin taurarin ’yan wasanta, wato Lionel Messi.

Haka kuma wannan lamari dai bai yi wa PSG dadi ba, inda za ta fafata daya daga cikin manyan wasanninta na gasar Ligue 1 wanda za ta je bakunta gidan Lyon ranar 9 ga watan Janairu ba tare da Pochettino da kuma Messi ba.

Messi wanda ya yi hutunsa na bikin Kirsimeti a kasarsa ta Argentina, zai ci gaba da zama a can har sai ya warke la’akari da dokokin da mahukunta suka gindaya na hana masu dauke da cutar yin tafiye-tafiye.