✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mene ne taimakon farko da za a ba wa wanda kunama ta harba?

Harbin yana da zafi sosai fiye da na maciji.

Harbin kunama ya fi faruwa a hannu da kafa fiye da kowane sashi na jiki, domin a mafi yawan lokuta hannu ko kafa ake kaiwa wurin da take boye, ta yadda ba tsammani sai dai kawai a ji harbin.

Kuma ta kan harbi kowa manya da yara, mata da maza, sai dai illar harbin ta fi yawa ga yara, musamman idan mai dafi ce.

Harbin yana da zafi sosai fiye da na maciji, ta yadda mutum zai iya kwala ihu ma bai sani ba don zafi, wurin zai ci gaba da zugi har sai an sa magani.

Idan irin haka ta faru akan kawo mutum asibiti domin ba da magani, inda akan yi wa mutum allurar kashe zugi a wurin.

Idan kunama ta harbi mutum, nan da nan wurin ya kan dauki zafi da radadi, a wasu lokuta ma har da kumburi ko zubar da jini daga wurin.

Idan harbin ya yi tsanani har dafi kunamar takan sa wa mutum, wanda dafin yakan sa a galabaita sosai ko ma a rasa rai.

Don haka idan aka samu irin haka za a samu wurin a wanke, idan yana zubar da jini a samu kyalle mai tsabta a daure wurin kafin a tafi asibiti domin gudun shigar dafi.

Mutanen gari da wuya su iya gane kunama mai dafi a cikin kunamu, don haka ne ake so ko an yi taimakon gaggawa dole a kai mutum asibiti tare da kunamar da ta yi harbin (bayan an kashe ta) domin a tantance ko mai dafi ce ko marar dafi, a kuma ajiye wanda ta harba a asibiti domin jiran ko-ta-kwana.

Jiran ko-ta-kwana yana nufin a dan kwantar da mutum na yini guda ko kwana guda domin kada alamun shigar dafi su bayyana.

Alamun shigar dafin sukan fara ne da dalalar miyau da sarkewar numfashi da shiga wani yanayi na suma da sauransu.

Da zarar alamun sun bayyana, akan samo maganin dafin a ba marar lafiyan abubuwa su lafa.

Sai dai kuma har yanzu bincike ya nuna a kasar nan babu allurar karya dafin kunama.

A kasashen da suka ci gaba, idan aka kawo wanda kunama ta harba asibiti, kusan dole ne a yi masa allurar karya dafin kunama nan take, ko ana tunanin dafi ya shiga ko bai shiga ba, saboda a kiyaye halin da marar lafiya zai shiga, kuma tunda allurar ba cutarwa take ba.

Za a iya kiyaye harbin kunama ta yin hankali idan za a shiga daji sarar itace da saka safar hannu ta roba da ta kafa idan za a shiga cikin itatuwa ko idan za a sa hannu a wani rami ko cikin wasu tarin itatuwa. Sai kuma yawan kula da yara sosai idan suna wasanni a cikin ciyawa.